Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyar agaji ta Save the Children ta koka game da karuwar cutar shan inna a Sudan ta Kudu
2020-11-03 11:58:50        cri
Kungiyar agaji ta duniya ta Save the Children, ta bayyana damuwa game da karuwar yara masu kamuwa da cutar shan inna a Sudan ta Kudu, lamarin da ke kara barazana ga rayuwarsu.

Kungiyar ta ce an samu sabbin yara 9 da suka kamu da cutar a Sudan ta Kudu, watanni 3 bayan hukumar lafiya ta duniya ta ayyana kawo karshen cutar baki daya a nahiyar Afrika.

Daraktar kungiyar a Sudan ta Kudu Rama Hansraj, ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, an samu barkewar cutar ce sakamakon karancin karfin garkuwar jiki da karancin riga kafi a al'ummomin, maimakon matsalar allurar riga kafi.

Ta ce karuwar masu kamuwa da cutar na haifar da damuwa matuka game da kara yaduwarta a kasar, lamarin da ya zama karin matsala baya ga karancin tsafta da cibiyoyin kiwon lafiya.

Karuwar adadin ya haifar da fargabar cewa, ko da wasu iyaye sun yi wa 'ya'yansu riga kafi, cutar ka iya yaduwa saboda rashin tsafta a galibin sassan kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China