Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Nijeriya za ta fitar da dala miliyan 13 domin tallafawa bangaren sufurin jiragen sama
2020-11-03 10:16:08        cri
Ministan kula da sufurin jiragen sama na Nijeriya Hadi Sirika, ya ce gwamnatin kasar ta amince da fitar da naira biliyan 5, kwatankwacin dala miliyan 13, a matsayin tallafi ga bangaren sufurin jiragen sama, domin saukaka tasirin annobar COVID-19 kan bangaren.

Da yake jawabi yayin wani zama a majalisar dokokin kasar jiya, a Abuja, Hadi Sirika ya ce bangaren yana da matukar muhimmanci, don haka ba zai yuwu ya durkushe ba.

A cewarsa, kamfanonin jiragen sama dake kasar za su samu naira biliyan 4 yayin da sauran harkokin kasuwanci na bangaren, za su samu naira biliyan 1.

Ya bayyana bangaren a matsayin mai muhimmanci ga ci gaban tattalin arzikin kasar da ma sauran kasashe, kuma tallafin na da nufin saukaka mawuyacin halin da suka shiga da ya sa biyan albashi ya zama matsala.

Tallafin na gwamnati na zuwa ne watanni bayan filayen jiragen saman kasar sun kasance rufe saboda annobar COVID-19.

A cewar wani rahoto da wata kafar yada labarai ta kasar ta fitar a jiya, kungiyar masu harkokin sufurin sama ta kasa da kasa, ta yi kiyasin 'yan Nijeriya 124,000 dake bangaren na cikin barazanar rasa ayyukansu saboda annobar. (Fa'iza Msutapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China