Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An Yi Bikin Matasan Sin Da Afirka Karo Na 5
2020-11-02 14:28:02        cri


Kwanan baya, an yi bikin matasan Sin da Afirka karo na 5 mai taken "Hada kai don gina makoma mai haske, da raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka zuwa sabon zamani" a birnin Beijing da lardin Jiangxi na kasar Sin.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, da Asusun Soong Ching Ling na kasar Sin, wato SCLF, da gwamnatin lardin Jiangxi ne suka shirya wannan biki cikin hadin gwiwa, domin kafa wani dandalin karfafa mu'amalar dake tsakanin matasan Sin da Afirka, da zurfafa dadadden gargajiyan dake tsakanin bangarorin biyu, ta yadda za a gina makoma mai haske ga matasan Sin da Afirka bai daya.

A jawabin da ya gabatar yayin bikin, wani wakili daga kasar Zimbabwe ya bayyana cewa, Sin da Afirka suna da dadadden zumunci mai karfi a tsakaninsu, kuma 'yan uwan juna ne. A nan gaba, matasan Sin da Afirka za su yi hadin gwiwa domin neman ci gaba, da kuma ba da gudummawasu wajen karfafa dunkulewar dukkanin al'ummomin Sin da Afirka.

Jawabin da ya gabatar ya samu amincewar mahalarta bikin kwarai da gaske, inda suka yi tafa masa.

A bikin da aka yi a birnin Beijing, wakilan da suka halarci bikin, sun ziyarci majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin, inda suka yi shawarwari da wasu mambobin majalisar, lamarin da ya sa su kara fahimtar halin da kasar Sin take ciki, musamman ma game da manufar hadin gwiwar jam'iyyu daban daban da manufar ba da shawara kan harkokin siyasa dake karkashin jagorancin Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, wato JKS.

Sa'an nan, wakilan Sin da Afirka kimanin dari daya, sun halarci taron tattaunawar masatan Sin da Afirka mai taken "Hadin gwiwar matasan Sin da Afirka, da sabuwar makomar dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka". Daga bisani kuma, sun halarci shirye-shiryen karawa juna sani game da al'adun gargajiyar Sin da cibiyar musayar kimiyya da fasaha da al'adu ta matasa ta Soong Ching Ling ta kasar Sin ta tsara, inda suka yin gwaji na wasan kwaikwayon gargajiyar Beijing na kasar Sin, da fasahar samar da ti da dai sauransu.

A lardin Jiangxi kuma, wakilan sun kai ziyara yankin nune-nunen tsohon murhu da al'adun al'umma na kauyen Jingde, da dakin kayayyakin fadi-ka-mutu na kasar Sin dake kauyen Jingde, da kuma titin yawon shakatawa na Tao Xi Chuan, domin kara fahimtar fasahohin kayan fadi-ka-mutu da yin mu'amala da masu aikin kera kayan fadi-ka-mutu na kasar Sin.

Bayan ziyararsu a wadannan wuraren, wani wakili ya bayyana cewa, mun kara fahimtar tarihin fasahohin kayan fadi-ka-mutu, da wannan al'adu na musamman. Sa'an nan, ya kara da cewa, "a da, ban taba ganin kayayyakin kade-kade na fadi-ka-mutu ba, amma, a wannan karo, ba kawai na ga yadda ake kade-kade da kayayyakin fadi-ka-mutu ba, har ma, na gwada da kaina, abin da ya ba ni sha'awa, kuma ba zan manta ba".

Haka kuma, wakilan sun kai ziyara a dakin nune-nunen kimiyya da fasahar jiragen sama masu saukar ungulu da yankin raya fasahohin VR. Wani wakilin daga kasar Chadi ya ce, ya karu sosai game da bunkasuwar harkokin kimiyya da fasahar kasar Sin, musamman ma game da fasahar VR, ya nuna fatan cewa, kasar Sin za ta samar da wadannan kyawawan fasahohi zuwa kasashen Afirka, domin tallafawa al'ummomin nahiyar Afirka.

Bugu da kari, wakilan sun kai ziyara a sansanin shuka lemon tanjarin dake kauyen Yijiahe, a wannan wuri, an yi musu bayani game da harkokin noma, da sakamakon da aka cimma a fannin kawar da talauci ta hanyar shuka 'ya'yan itatuwan tanjarin da dai sauransu.

Bayan ziyarar tasu a wannan wuri, wakilan sun nuna yabo matuka game da dabarun da aka tsara wajen kawar da talauci a wannan wuri, kamar kafa cikakken tsarin shuka, da samar wa, da sayar da tanjarin, da raya harkokin yawon shakatawa bisa bunkasuwar ayyukan gona da sauransu.

Wani wakili ya ce, abin da ya burge shi matuka ba zakin tanjarin da ya dandana ba, sai yadda wannan 'ya'yan itatuwa ya samar da bunkasuwar tattalin arziki ga wannan kauye.

Bisa kokarin da bangarori daban daban suka yi, an yi nasarar shirya bikin matasan Sin da Afirka sau hudu, tun da aka fara gudanar da bikin a shekarar 2016. A halin yanzu, bikin ya kasance muhimmin dandalin zurfafa zumuncin dake tsakanin matasan Sin da Afirka da karfafa mu'amalar dake tsakaninsu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China