Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin kasar Zimbabwe: Bude kofar kasar Sin zai amfanawa dukkan kasashen duniya
2020-10-31 17:12:20        cri

 

Taron cikakken zama na 5 na kwamitin tsakiya na 19 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da aka kammala ba da dadewa ba, ya ja hankalin kasashe daban daban. A wata hira da ya yi da manema labaru na babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG a takaice, Donald Rushambwa, manazarcin cibiyar binciken musayar tattalin arziki da al'adu ta kasar Sin da Afirka ta Zimbabwe, ya yaba sosai da nasarorin ci gaban da kasar Sin ta samu a lokacin shiri na shekaru 5 karo na 13, kuma yana cike da fata kan shiri na shekaru 5 na 14. Ya yi imanin cewa, ci gaba da bude kofa da kasar Sin ke yi, zai amfanawa kasashen duniya, ciki har da kasashen Afirka.

Donald Rushambwa ya yi karatun digiri na biyu a kasar Sin daga shekarar 2014 zuwa 2019, kuma ya zama malamin ziyara wato malami mai zuwa lokaci zuwa lokaci. Domin bukatun nazari, ya taba gudanar da bincike a larduna da yawa na kasar Sin, inda ya ga manyan sauye-sauye a sassa daban-daban na kasar Sin a lokacin "Shirin shekaru 5 na 13".

Donald Rushambwa ya yi tsokaci game da fadada ayyukan bude kofa da kasar Sin ke yi. A ganinsa, matakin zai amfani dukkan kasashen duniya, ciki har da Zimbabwe. Ya fadawa manema labarai cewa, ba za a iya aiwatar da shirin kashin kai ba, sai ta hanyar bin ra'ayin bangarori da dama tare da karfafa hadin gwiwar kasa da kasa, inda ya ce ta haka ne za a iya inganta cinikayyar duniya, ta yadda za a amfanawa dukkan kasashe gaba daya. (Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China