Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sabon tsarin ci gaban kasar Sin ya samar da sabuwar dama ga duniya
2020-10-31 17:01:43        cri

 

Zaman taro na 5 na kwamitin tsakiya na 19 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda aka rufe a ranar 29 ga watan Oktoba, ya yi nazari tare da amincewa da "shawarwarin da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin ya gabatar kan tsara shirin shekaru 5 karo na 14 don ci gaban tattalin arzikin kasa da zamantakewar al'umma da burin da ake son cimmawa kafin shekarar 2035", wanda ba nuna makomar kasar Sin, da hanyar da kasar za ta bi kadai ya yi ba, har ma da tabbatar da kawo sabbin damarmaki ga farfadowar tattalin arzikin duniya da ci gabanta.

Sanarwar da aka fitar ta tabbatar da cewa, bada muhimmanci ga inganta ci gaba mai inganci, da zurfafa yin kwaskwarima kan tsarin samar da kayayyaki, da mayar da dogaro da kai a fannin kimiyya da fasaha matsayin ginshikin bunkasa kasa, da fadada bukatun cikin gida a matsayin tushe, musamman mayar da hankali kan raya tattalin arziki a cikin gida, don ganin an iya hade kasuwar cikin gida da ta ketare domin samun ci gaba mai karfi da dorewa, sun bayyana muhimman fannonin da za a mai da hankali kansu, wanda ke da matukar ma'ana ga kasar Sin da duniya baki daya.

 

 

"Sabon tsarin ci gaba" na kasar Sin bai nanata bunkasa tattalin arzikin cikin gida kadai ba, a maimakon haka, ya bada muhimmanci kan hade kasuwar cikin gida da ta ketare. A zahiri, tun bayan rikicin kudi na kasa da kasa na shekarar 2008, kasar Sin ta samu ci gaba matuka wajen sake daidaita tattalin arziki, bunkasar tattalin arzikin kasar yana ta kara dogaro da sayya a cikin gida da saka jari.

Kasuwa abu ne da ake nema a duniya. Kasar Sin dake samun karfin ci gaban tattalin arziki a cikin gida, wadda ke da babbar kasuwa, babu makawa za ta jawo karin albarkatu masu inganci a duniya, haka zai haifar da zirga-zirgar tattalin arzikin kasa da kasa, da kara hade kasuwar cikin gida da ta ketare domin samun ci gaba mai karfi da dorewa.

Abin lura a nan shi ne, an zartas da shawarar kan dogon burin da ake son cimmawa nan da shekarar 2035 a wajen babban taro na 5 na kwamitin tsakiya na 19 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda ke nuna cewa ci gaban kasar Sin na da zango mai tsawo, kuma yakinin da ya kawo wa duniya shi ma zai kasance na dogon lokaci, wanda ke nuna yadda Sin take daukar sauke nauyin dake wuyanta a matsayin wata babbar kasa. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China