Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kogin da al'ummar Sinawa ke dauka a matsayin uwa
2020-10-30 20:55:09        cri





Kasar Sin na daya cikin kasashen da suka fi yawan koguna a duniya. Sai dai daga cikin dimbin kogunan, akwai wani da al'ummar kasar suke daukarsa a matsayin uwa, a sakamakon yadda kaka da kakaninsu suka fara rayuwa a shiyyar da kogin ya ratsa, inda kuma suka fara samun wayewar kansu, kogin da ake kira rawayen kogi, ko kuma yellow river a Turance.

A sakamakon muhimmancinsa ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya dora matukar muhimmanci a kan kiyaye muhallin shiyyar da kogin ya ratsa tare kuma da inganta bunkasuwar shiyyar. Har ma a cikin shekaru biyu da suka wuce, ya kai rangadi wasu larduna da jihohi shida da kogin ya ratsa, inda ya gabatar da matakan da ya kamata a dauka wajen kiyaye kogin da kuma bunkasa shiyyar da kogin ya ratsa.

Birnin Lanzhou, hedkwatar lardin Gausu na kasar Sin, ya kasance birnin da rawayen kogi ya ratsa. A watan Satumban bara, shugaba Xi Jinping wanda ya kai rangadin birnin, inda ya samu fahimtar yadda ake daidaita yanayin kogin da kuma ba shi kariya. Ya kuma yi nuni da cewa, babban aikin da ya kamata al'ummar Sinawa suka gudanar shekara da shekaru shi ne su kiyaye kogin da suke dauka a matsayin uwa, kasancewar lardin Gansu bangare na farko na kogin, ya kamata ya dauki nauyin gyara muhallin yanayin bangaren na kogin, tare da kare shi daga gurbacewar muhalli, kuma ya kamata birnin Lanzhou ya yi jagora a fannin kiyaye ingancin ruwan kogin.

To, shin yaya rawayen kogin ya kasance, kuma shin kuma yaya birnin Lanzhou? An ce, waka a bakin mai ita ta fi dadi, don haka a cikin shirinmu na yau, mun samu damar tattaunawa tare da malam Samaila Usman, dan Nijeriya da ke dalibta a birnin, don ya ba mu karin haske.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China