Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya yi jawabi a taron karawa juna sani da JKS ta shirya don sauraron ra'ayin wadanda ba 'yan jam'yyar ba game da daftarin shirin raya kasa
2020-10-30 20:17:58        cri
Xi Jinping, babban sakataren kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS), ya gabatar da wani muhimmin jawabi, yayin wani taron karawa juna sani da jagororin jam'iyyar suka shirya, domin neman ra'ayoyin wadanda ba mambobin jam'iyyar ba, kan yadda za a tsara daftarin shirin raya tattalin arziki da jin dadin al'ummar Sinawa.

Xi ya jagoranci taron karawa juna sanin da aka gudanar kwanan baya, domin tsara daftarin shawararin da kwamitin kolin JKS ya gabatar, inda za a fito da shirin raya tattalin arziki da jin dadin jama'a na shekaru biyar karo na 14, wanda za a aiwatar daga shekarar 2021 zuwa ta 2025, da manufofin da ake fatan aiwatarwa na dogon lokaci nan da shekarar 2035.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China