Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararren Nijeriya: dandalin FOCAC ya ba da gudummawa ga bunkasuwar kasashen Afirka
2020-10-30 12:14:06        cri

A ranar 28 ga wata, shugaban cibiyar nazarin harkokin kasar Sin dake tarayyar Nijeriya Charles Onunaiju, ya fidda wani sharhi mai taken "Cika shekaru 20 da kafuwar dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC: batutuwa da makoma" a jaridar "Daily Trust" ta Nijeriya. Cikin sharhin na sa, malam Onunaiju ya bayyana cewa, dandalin FOCAC shi ne muhimmin dandali na habaka shawarwarin dake tsakanin bangarori daban daban. Cikin shekaru 20 da suka gabata, sakamakon da aka cimma cikin tarukan dandalin FOCAC ya ba da gudummawa ga sassan nahiyar Afirka a fannin raya tattalin arziki da zaman al'umma, lamarin da ya samar da makoma mai haske ga al'ummomin nahiyar Afirka.

Haka kuma, ya ce, bayan kafa dandalin FOCAC, kasar Sin ta kara ba da taimako ga kasashen Afirka wajen raya harkokinsu, inda adadin musayar cinikin dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ya ninka sau 20 cikin wadannan shekaru 20. Kasar Sin ta zama abokiyar ciniki ta kasashen Afirka a matsayi na farko cikin shekaru 11 a jere. Kuma gaba daya, ta zuba jari na dalar Amurka biliyan 110 kai tsaye a kasashen Afirka, kana kamfanoni kimanin dubu 4 na kasar Sin, sun raya masana'antunsu a sassan kasashen Afirka.

Bugu da kari, layukan dogon da kamfanonin kasar Sin suka ba da taimako ga kasashen Afirka wajen ginawa, sun kai tsayin sama da kilomita dubu 6, kuma sun ba da taimako ga kasashen Afirka wajen gina tashoshin jiragen ruwa kimanin guda 20, da manyan na'urorin samar da wutar lantarki sama da gudu 80, wadanda dukkansu suka ba da muhimmiyar gudummawa ga bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afirka, da raya harkokin masana'antu a kasashen, ta yadda, za su nemi ci gaba da kansu.

Ya ce bisa kokari da hadin gwiwar Sin da Afirka, ana ci gaba da raya dandalin FOCAC bisa shawarar "Ziri daya da hanya daya", tabbas ne, a nan gaba, dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu za ta ci gaba da samun kyautatuwa kamar yadda ake fata. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China