Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bai Dace Manyan Kasashe Su Rika Tilasawa Saura Zabar Manufofin Gudanarwa Ba
2020-10-29 16:35:00        cri

A gabar da mafi rinjayen kasashen duniya ke kiraye-kirayen bunkasa hadin gwiwa, da cudanya bisa dokokin kasa da kasa, kasashen yammacin duniya musamman Amurka, na ci gaba da daukar matsaya ta kashin kai, tare da yiwa kananan kasashen duniya "hannun ka mai sanda", a wasu lokuta ma har da matsin lamba game da yadda za su rika tafiyar da alakar su da sauran kasashe.

Wasu rahotannin baya bayan nan sun nuna cewa, kafin sakataren wajen Amurka Mike Pompeo ya isa kasar Sri Lanka don ziyarar aiki, ana hasashen Amurkan za ta bukaci Sri Lanka ta aiwatar da wasu manufofi masu nasaba da alakarta da Sin.

Bisa wadannan rahotanni, ana iya ganin yadda Amurka ke amfani da karfin fada a ji kan kanana da matsakaitan kasashe, tana umartar su da daukar wasu matakai, wadanda ba lallai ne su zamo masu amfani gare su ba.

Sanin kowa ne cewa, karkashin manufofin karfafa alakar sassan biyu, wato bunkasa zaman jituwa, da hadin gwiwa don cimma gajiya tare, da fadada moriyar al'ummun su, Sin da Sri Lanka na kara kyautata zaman karko yadda ya kamata. Ke nan duk wani yunkuri na gurgunta wannan kyakkyawar alaka dake tsakanin sassan biyu, ba komai ba ne illa gyeta, da burin lalata zumunta mai inganci.

Tuni ma dai su kan su al'ummun kasar Sri Lanka, suka fara nuna rashin amincewa da wannan mataki na Amurka, inda a kwana baya, wani jami'in diflomasiyyar kasar ya rubuta wata Makala wadda ke cewa, kasar sa za ta ci gaba da aiwatar da manufofin ta na cudanya da kasashen waje ne daidai da tanajin kundin tsarin mulkin kasa, bisa dokokin da al'ummar kasar suka amincewa, kuma ba sa bukatar wata kasa ta waje, ta koya musu yadda za su gudanar da cudanya da sauran kasashen duniya.

Ko shakka babu, irin wadannan kalamai, suna da karfafa gwiwa, tare da kara shaida yadda sassan duniya ke da burin dunkulewa, da inganta yin hadin gwiwa mai ma'ana, wanda hakan ke nuna tabbas, yinkurin masu son haifar da baraka zai ci tura. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China