Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bangarori daban daban na daukar matakan share fagen bikin CIIE karo na 3 da za a yi a watan Nuwamba
2020-10-29 12:13:47        cri

A gabannin bikin baje kolin kayayyakin da ake shigarwa kasar Sin karo na uku CIIE da za a yi a watan Nuwamba mai zuwa, a lokacin da ake daukar matakai na yau da kullum na rigakafin sake bullar cutar COVID-19 a kasar, bangarori daban daban sun dauki matakai masu tarin yawa na taimakawa wajen shirya bikin baje kolin kamar yadda ya kamata. A yayin bikin, an kafa yankuna 6 na nune-nunen kayayyaki iri daban daban, kamar su, yankin kayayyakin abinci da amfanin gona, da yankin motoci, da yankin na'urorin fasaha, da yankin kayayyakin masarufi, da yankin na'urorin jinya da magunguna, da yankin ba da hidima. Tun daga ranar 26 ga watan Oktoban, an fara kawata wadannan yankuna 6, har ma an kusan kammala aikin kawata yankin nune-nunen na'urorin fasaha, da na motoci da na na'urorin jinya da magunguna.

Saboda har yanzu ana namijin kokarin dakile annobar cutar COVID-19 a duk fadin duniya, yankin nune-nunen na'urorin jinya da magunguna ya fi jawo hankulan jama'a, wato kawo yanzu, kamfanonin cikin gida da na waje gaba daya guda 340, ciki har da manyan kamfanoni fiye da 70 wadanda suka fito daga kamfanoni 500 mafi karfi a duk fadin duniya, sun halarci wannan bikin. Bisa batun rigakafi da kuma shawo kan annobar COVID-19 da ya fi jawo hankulan jama'a, an kebe wani yankin musamman na nune-nunen kayayyakin rigakafi da kuma shawo kan annobar. Madam Cao Pei, wadda ke kula da aikin janyo hankalin 'yan kasuwa da su halarci wannan bikin CIIE karo na uku, tana mai cewa, "Sakamakon annobar COVID-19 da take yaduwa a duk duniya, an fi maida hankali kan batun rigakafi da shawo kan annobar. Sakamakon haka, mun kebe wani fili domin nune-nunen kayayyakin kiwon lafiyar jama'a musamman a cikin yankin nune-nunen na'urorin jinya da magunguna. Kawo yanzu, manyan kamfanoni da yawa wadanda suke sahun gaba a fannin kiwon lafiya a duniya za su kafa rumfunansu a wannan filin musamman."

Wannan bikin CIIE karo na uku, wani bikin cinikayya ne na kasa da kasa wanda kasar Sin ta sake shiryawa a lokacin da har yanzu ake yaki da cutar COVID-19. Bisa ka'idar yin rigakafi da shawo kan cutar da hukumar shirya bikin ta gabatar, kafin a shigar da kayayyaki wajen bikin, dole ne za a fesa maganin kashe kwayoyin cuta a kan kunshin kayayyakin, da kuma tabbatar da ganin motoci da mutane da kayayyaki da za a shigar da su wajen biki babu wata matsala. Mr. Peng Chunyan, mai taimakawa babban direktan cibiyar tafiyar da babban dakin baje koli na kasa da kasa na Shanghai ya bayyana cewa, "Ana fesa maganin kashe kwayoyin cuta sau daya da safe, sannan a fesa maganin sau daya da maraice ga iska a kowace rana. Bugu da kari, za mu fesa maganin kashe kwayoyin cutar ga kunshin kayayyakin da za a yi nune-nunensu a yayin bikin."

A gabannin kaddamar da bikin, hukumomin shirya bikin sun kuma dauki matakai daban daban na bada hidimomi ga bikin. A ranar 27 ga watan, bankin shigi da fici na kasar Sin ya fitar da shirin bada hidimar hada-hadar kudi, inda ya shelanta cewa, bankin ya kebe kudin Sin RMB yuan biliyan 350 domin tallafawa kayayyakin da za a shigar da su kasar Sin. Mr. Dai Shihong, babban direktan sashen bada hidima na bankin ya yi bayani cewa, "Baya ga 'yan kasuwa wadanda suke fitar ko shigar da kayayyaki, za kuma mu tallafawa kamfanoni wadanda suke ba da hidima ga 'yan kasuwa wadanda suke fitar da ko shigar da kayayyaki kasar Sin."

A waje daya, game da aikin binciken annoba kan kayayyakin da ake shigi da ficin, Mr. Wang Jun, babban direktan sashen sa ido kan tasoshin ruwa na babbar hukumar kwastam ta kasar Sin, ya bayyana cewa, za a dauki sabbin makatan binciken kayayyakin da ake shigar da su bikin CIIE karo na uku, kuma za a kara nuna goyon baya ga 'yan kasuwa wadanda suke shigo ko fitar da kayayyaki ta shafin intanet. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China