Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsawon rayuwar Sinawa ya karu da kusan shekara guda
2020-10-28 21:18:32        cri
A yau ne ofishin labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya shirya wani taron manema labarai, game da gyare-gyaren da aka aiwatar da ma ci gaban da aka samu a fannin lafiya, a yayin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 13.

Rahotanni na nuna cewa, yayin aiwatar da wannan shiri, matsakaicin tsawon rayuwar Sinawa ya karu daga shekaru 76.34 a shekarar 2015 zuwa shekaru 77.3 a shekarar 2019, kana yawan mace-mace mata masu juna biyu ya ragu daga kaso 20.1 cikin dubu 100 zuwa kaso 17.8, sai kuma mutuwar jarirai da shi ma ta ragu daga kaso 8.1 cikin dubu zuwa kaso 5.6, yayin da mutuwar yara 'yan kasa da shekaru biyar ita ma ta ragu daga kaso 10.7 cikin dubu zuwa 7.8 daga shekarar 2015 zuwa shekarar 2019 (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China