Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shirin raya kasa da Sin ta tsara zai haifar da damammakin ci gaba ga duniya
2020-10-28 13:24:31        cri

A kwanakin nan ana gudanar da cikakken zama na 5 na kwamitin tsakiya na 19 na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, inda manyan kusoshi na jam'iyyar, masu raki da ragamar mulki a kasar Sin, suke tantance shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14, gami da burin raya kasa nan da shekarar 2035. To amma shin ko wane irin tasiri wannan taro zai haifar ga al'ummun kasashe daban daban?

Don sanin tasirin shirin raya kasa na shekaru 5 da kasar Sin ta tsara, da farko dai za mu iya duba tasirin da shirin raya kasa na shekaru 5 na 13, wanda ya kayyade ayyukan raya tattalin arziki tsakanin shekarun 2016 da 2020 ya haifar. A cikin wadannan shekaru 5, jimillar kudin kayayyakin da ake samarwa a gida, wato GDP na kasar Sin, yana ta karuwa, lamarin da ya sa ake samun karin guraben aikin yi a kasar, da karin kudin shiga ga al'ummar kasar. Alal misali, cikin shekaru 5 da suka wuce, an samar da karin guraben aikin yi ga mazauna birane da ya zarce miliyan 60. Kana ana samar da kudin alawus ga tsoffin kimanin miliyan 30. Ya zuwa karshen shekarar 2019, an samar da gidajen kwana ga marasa karfi fiye da miliyan 38, wadanda suke hayarsu da kudi mai rahusa.

Duk dai a shekarar 2019, tsawon rayuwar jama'ar kasar Sin ya kai shekaru 77.3, kana ana samar da hidimar ishorar lafiya ga fiye da kashi 95% na al'ummar kasar. Yayin da yawan marasa karfi dake cikin al'ummar kasar ya sauka daga kashi 5.7% na shekarar 2015, zuwa kashi 0.6% na shekarar 2019.

Yanzu haka a kasar Sin, wadda yawan al'ummarta ya kai biliyan 1.4, yawan GDPn mutum guda ya wuce dalar Amurka dubu 10, saboda haka kudin shiga na jama'ar kasar ya karu sosai, abin da ya sa bukatunsu game da nagartattun kayayyaki na kasashe daban daban su ma suka karu sosai. A shafunan Internet na masu sayar da kayayyaki na kasar Sin, za a iya ganin cewa, wasu abinci, da kayayyakin fasahohin zamani, kirar sauran kasashe, suna samun karbuwa sosai, inda jama'ar kasar ke ta kokarin sayen da yawansu a kowace rana.

Bisa wadannan ci gaban da aka samu, za mu iya hasashen matakai na raya kasa da kasar Sin za ta gabatar a wannan karo, da kuma tasirin da za su samar ga sauran kasashe.

Da farko dai, sabuwar manufar raya kasa ta kasar Sin, za ta shafi batun kyautata zaman rayuwar jama'ar kasar. Da ma dai, wata babbar manufar kasar Sin a fannin mulki ita ce "mai da moriyar jama'a gaban komai". Saboda haka, cikin sabuwar manufar da za a gabatar a wannan karo, za a dora cikakken muhimmanci kan raya fannoni ilimi, da kiwon lafiya, da samun gidajen zama, da gina ingantattun kayayyakin motsa jiki, don su amfani jama'ar kasar. Ban da wannan kuma, za a aiwatar da dabarun daidaita wasu matsalolin da kasar Sin take fuskanta a fannan tattalin arziki. Misali, rashin daidaito tsakanin yankunan gabas da yamma a fannin samun ci gaban tattalin arziki, da bambancin ci gaban birane da kauyuka, da rashin kwarewar kirkiro sabbin fasahohi, da dai makamantansu.

Sa'an nan, idan mun dubi yanayin da duniyarmu ke ciki, za a gano cewa, bazuwar annobar COVID-19 ta sa ana samun wani sauyin yanayi a duniya, inda ake fama da koma bayan tattalin arziki, da wasu matakan da ake dauka na kashin kai, da kokarin kare kai maimakon kula da saura.

Duk da haka, kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da babbar manufarta ta bude kofarta ga sauran kasashe daban daban. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba fadin cewa, za a yi kokarin hadin gwiwa da duk wata kasa, ko yanki, ko kuma kamfani, wanda ke son hadin kai tare da kasar Sin, ta yadda za a samar da wani tsari na buda kofa da hadin gwiwa, wanda ya shafi fannoni, da salon aiki daban daban. Hakan ya nuna cewa, Sinawa za su ci gaba da kokarin kyautata zaman rayuwarsu, kana kasar Sin za ta ci gaba da kokarin bude kofar kasuwanninta ga sauran kasashe. Ban da wannan kuma, kasar Sin za ta ci gaba da kokarin ciniki, da mu'amala tare da kasashe daban daban. Kasar Sin za ta more da damammaki na ci gaba tare da sauran bangarorin duniyarmu. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China