Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gudanar da taron cinikin amfanin gona tsakanin Sin da Afirka ta yanar gizo cikin nasara
2020-10-28 10:54:45        cri
Bankin masana'antu da ciniki na Sin wato ICBC, da rukunin bankuna ta kasar Afirka ta Kudu, da kuma kamfanin kasuwanni na Gaoqiao na lardin Hunan na kasar Sin, sun gudanar da taron cinikin amfanin gona a tsakanin Sin da Afirka na shekarar 2020 ta yanar gizo, inda aka samu halartar kamfanoni sama da 40.

A gun taron na jiya wanda ya kammala cikin nasara, an gudanar da cinikin amfanin gona kamar su kofi, da coco, da coconut, da ridi da sauransu, an kuma cimma yarjejeniyoyin hadin gwiwa fiye da 40.

Kamfanonin kasashen Afirka masu halartar taron sun bayyana cewa, bukatun kasuwa na kasar Sin, sun samar da babbar dama gare su. Gudanar da taron cinikin a wannan karo ta yanar gizo, zai kara kawo damar ciniki ga hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka. (Zainab Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China