Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamata ya yi munafukan Amurka "masu rajin kare muhalli" su yiwa duniya bayani
2020-10-27 20:59:02        cri

 

Kwanan nan, wasu 'yan siyasan Amurka suna ta tallata batun sauyin yanayi da kuma batun kare muhalli saboda burinsu na siyasa, kuma sun sha takala da neman bata sunan kasar Sin da nufin dora laifi kan kasar da kuma boye gazawarsu a fagen muhalli. Amma, irin wannan mataki na "barayin da ke kira da kama barayi" ba kawai ya kasa yaudarar duniya ba ne, har ma ya ba wa al'ummomin duniya damar kara fahimtar cewa, yadda wadannan 'yan siyasar Amurka dake kiran kansu "masu rajin kare muhalli" ke "sauya tarihi," da gujewa nauyin dake bisa wuyansu na kasa da kasa, da kuma gurgunta tsarin tafiyar da muhalli na duniya.

Janyewa daga yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, kasa cika alkawuran da ta dauka kan harkokin kasa da kasa, ba sa cikin yarjeniyoyin muhalli da dama a fannoni daban daban, na hana aiwatar da yunkurin kiyaye muhalli tsakanin bangarori da dama……Takardu biyu na "Jerin bayanan lalata muhalli na Amurka" da "Rahoton matakan lalata yanayin duniya" da aka fitar a shafin yanar gizon ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin a kwanan nan, tare da hujjoji da bayanan da ba za a iya musuntawa ba, sun bayyana munanan ayyukan da kasar Amurka ta yi a fannin muhalli. Dangane da wadannan shaidu masu karfi, ta yaya 'yan siyasan Amurka za su nemi bata sunan wasu.

Duniya guda muke rayuwa. Hakki ne da ya rataya a wuyan dukkan kasashe daban daban su kare muhalli da inganta ci gaba mai dorewa. A hakika, wasu manyan kasashe da kungiyoyi, ciki har da kasar Sin da kungiyar Tarayyar Turai, suna nan suna amsawa tare da nuna goyon baya ga kiran da MDD ta yi, na tsara manufofin kiyaye muhalli bisa la'akari da moriyar dukkan bil Adama na dogon lokaci, tare kuma da ci gaba da sauke nauyin da ke kansu. A halin yanzu, kasar Sin ta cimma burin tinkarar matsalar sauyin yanayi na shekarar 2020 tun kafin lokacin da aka tsara kuma ta cika burinta. A babban taron muhawarar MDD karo na 75 da aka gudanar a ranar 22 ga watan Satumba, shugaban kasar Sin ya sanar da cewa, za ta rage hayakin carbon dioxide da kasar dake fitarwa nan da shekarar 2030, kuma za a yi kokarin daidaita hayakin na carbon da take fitarwa nan da shekarar 2060. Wannan sadaukarwa ce da alkawarin da kasar Sin ta yi don gina duniya mai tsabta da kyan gani wanda ya samu karbuwa sosai daga kasashen duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China