2020-10-27 19:30:34 cri |
Boss Mustapha wanda ya bayyana haka, yayin wani taron manema labarai da aka shirya jiya Litinin ya ce, a cikin makonni biyu da suka gabata, an gudanar da gagarumar zanga-zanga a sassa daban-daban na kasar, ba tare da martaba ka'idojin yaki da annobar COVID-19 ba.
Ya ce, baya ga yadda yanayin tsaron kasar ya shafi tattalin arziki da zaman takewar al'umma, gangamin da aka gudanar da ma yadda masu boren suka rika balle manyan dakunan ajiyar kayayyaki, da gidaje da wawashe dakunan ajiyar kayayyaki da matasa suka yi, ya jefa kasar cikin hadarin sake bullar kwayar cutar.
A cewar cibiyar kandagarkin yaduwar cututtuka ta kasar(NCDC), an tabbatar sabbin mutane 119 da suka kamu cutar a ranar Litinin, adadin da ya kai 62,111 gaba daya a kasar. Akwai mutane 1,132 da cutar da halaka, baya ga 57,571 da suka warke daga cutar, tun barkewarta a karshen watan Fabrairu.(Ibrahim)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China