Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Halayyar shugabannin Sinawa ya taka rawar bunkasuwar al'adun gargajiyar kasar
2020-10-26 20:45:56        cri

 

Wasannin gargajiya wani bangare ne daga cikin muhimmin hanyoyin samar da nishadi ga al'umma gami da kiyaye al'adun gargajiya da tarihin kowace al'umma. Ko shakka babu, shugabannin kasar Sin suna daukar batun raya al'adun gargajiya da muhimmancin gaske. Shugabanni dai su ne fitilun dake haskakawa al'umma hanya domin kaiwa ga gaci. Fannin raya wasannin gargajiya a kasar Sin yana matukar samun kulawa daga mahukuntan kasar yadda ya kamata. Wannan mataki ya taka muhimmiyar rawa wajen yiwa al'umma kaimi domin rungumar harkokin wasannin gargajiya tare da bunkasa su yadda ya kamata. Koda a karshen makon da ya gabata, sai da babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma shugaban kasar Xi Jinping ya amshi wata wasika wanda malamai da dalibai na kwalejin wasannin gargajiyar kasar Sin suka aike masa. Shugaban ya yaba da kokarin da suke nunawa don raya fasahar wasannin gargajiyar kasar ta Sin. Xi ya jaddada cewa, wasannin gargajiyar kasar Sin al'adun gargajiya ne masu daraja na kasar, ya dace malamai da dalibai na kwalejin wasannin gargajiyar kasar Sin su kara sanya kokari a daidai lokacin murnar cika shekaru 70 da kafuwar kwalejin domin ciyar da wasannin gaba. Bugu da kari, a kwanan baya ma, wasu wakilan malamai da dalibai na kwalejin wasannin gargajiyar kasar Sin sun rubuta wata wasika zuwa ga babban sakatare Xi, inda suka yi bayani kan sakamakon da suka samu a cikin shekaru 70 da suka gabata, tare kuma da nuna fatansu na raya wasannin gargajiyar kasar Sin.

Yadda mahukuntan kasar ke nuna kulawa da bayar da kwarin gwiwa ya taimakawa masu sha'awar harkokin wasannin gargajiyar nuna kwazo da tsayawa tsayin daka wajen ci gaban wannan fannin. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China