Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Masar ya sake sabunta dokar ta bacin da aka kakaba a kasar na watanni uku
2020-10-26 20:24:00        cri
Rahotanni daga kasar Masar na cewa, shugaban kasar Abdel Fattah al-Sisi, ya fitar da wata doka dake sabunta dokar ta bacin da aka kakaba a fadin kasar na karin watanni uku, daga yau Litinin.

Bisa kundin tsarin mulkin kasar ta Masar, wajibi ne sai majalisar dokokin kasar ta amince da shawarar da shugaban ya yanke ta sabunta wa'adin dokar ta bacin.

A watan Afrilun shekarar 2017 ne dai, shugaban ya fara ayyana dokar ta baci ta tsawon watanni uku a dukkan fadin kasar, biyo bayan hare-haren bam din da aka kai wasu majami'u biyu a lardunan Gharbiya da Alexandria dake arewacin kasar, hare-haren da suka halaka mutane a kalla 47, kana wasu sama da 120 kuma suka jikkata. An kuma sha sabunta dokar kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Kasar Masar dai, ta sha fuskantar ayyukan ta'addanci da suka kai ga halaka daruruwan 'yan sanda da sojoji, tun lokacin da aka hambarar da tsohon shugaban kasar Mohamed Morsi a shekarar 2013.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China