2020-10-25 15:41:31 cri |
Xu Bing, kakakin baje kolin ya ce, bikin na kwanaki 10 ya ja hankalin kamfanonin cikin gida da na kasashen ketare kusan 26,000, inda aka baje kolin kayayyaki sama da miliyan 2.47, daga ciki akwai sabbin kayayyaki 730,000.
Masu sayen kayayyaki daga kasashe da shiyyoyin duniya sama da 226 ne suka mika bukatar neman halartar bikin baje kolin, tare da gudanar da shawarwarin ciniki, kamar yadda mashirya bikin suka bayyana.
A lokacin baje kolin, an gabatar da ayyuka kai tsaye ta intanet 284,800 wanda ya ja hankali masu kallo kusan miliyan 1.9, kana kamfanoni 2,046 sun yi amfani da hanyar fasahar bidiyo wajen tallata hajojinsu, wanda ya ja hankali masu ziyara sama da 160,000.
Wannan shi ne karo na biyu da aka gudanar da baje kolin ta hanyar intanet a wannan shekara sakamakon barkewar annobar COVID-19.
Baje kolin wanda aka fara a shekarar 1957, an bayyana shi a matsayin wani muhimmin ma'auninn gwajin harkokin ciniki tsakanin kasar Sin da kasashen ketare. (Ahmad)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China