Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kowa da kowa na sauke nauyin kiyaye zaman lafiya bisa wuyansa
2020-10-24 15:28:19        cri

 

 

Yau Asabar 24 ga watan Oktoba, ranar MDD ce, wadda aka kebe ta a shekarar 1947, yayin babban taron MDD domin tunawa da "ka'idar MDD", babban taken ranar shi ne, kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin duniya, tare kuma da raya huldar sada zumunta dake tsakanin kasa da kasa, ta yadda za a ingiza bunkasuwar tattalin arziki da zaman takewar al'umma da al'adu ta hanyar gudanar da hadin gwiwa dake tsakanin kasa da kasa.

Kamar yadda tsohon babban sakataren majalisar Ban Ki-moon ya bayyana, MDD ba wurin taron jami'an diplomasiyya ba ne kawai, a cewarsa, majalisar na gudanar da aikin kiyaye kwanciyar hankali, da aikin ma'aikatar kiwon lafiya wadda ke raba magani, da aikin tallafawa 'yan gudun hijira, da kuma aikin kare hakkin dan Adama, ko shakka babu ayyukan da MDD ke gudanarwa suna da matukar ma'ana.

A don haka kasar Sin take son shiga dukkan shirye-shiryen da MDD ta tsara, musamman shirin kiyaye kwanciyar hankali a kasashen Afirka, saboda ana ganin cewa, kowa da kowa yana sauke nauyin dake wuyansa na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin duniya.

Hakika a ko da yaushe kasar Sin tana himma da kwazo domin shiga aikin kiyaye zaman lafiyar da MDD ke gudanarwa a nahiyar Afirka, har an yaba da ayyukan sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin kwarai. Alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, tun daga shekarar 1990, har zuwa yanzu, gaba daya kasar Sin ta shiga aikin kiyaye zaman lafiya a kasashen Afirka na MDD har sau 12, jami'an kiyaye zaman lafiya da kasar ta tura wa kasashen sun kai sama da dubu 3, musamman tun bayan shekarar 2003, kasar Sin ta kara habaka aikinta na kiyaye zaman lafiya a kasashen Afirka bisa shirin MDD, yanzu haka tana gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya guda bakwai a nahiyar, inda jami'an tsaron kasar Sin da yawansu ya kai 1271 suke gudanar da ayyuka a kasashen Kongo (Kimshasa) da Liberiya da Sudan da sauransu. A sa'i daya kuma, kasar Sin tana gudanar da hadin gwiwa tsakaninta da wasu kasashen Afirka a fannin aikin soja bisa dokokin da abin ya shafa.

Nan gaba kuma kasar Sin za ta ci gaba da sa kaimi ga sauran kasashen duniya domin su kara mai da hankali kan batutuwan dake shafar kasashen Afirka, ta hanyar samar da karin tallafin kudi, ta yadda za a daidaita hargitsin nahiyar yadda ya kamata.

Hakazalika, kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kokarin da kasashen Afirka suke yi domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, tare kuma da cimma muradun sassan biyu wato Sin da Afirka na sada zumunta da shimfida zaman lafiya da gudanar da hadin gwiwa da kuma samun ci gaba tare karkashin jagorancin MDD. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China