2020-10-23 11:13:44 cri |
A kwanakin baya ne babban darektan hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa, yanzu haka adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da annobar cutar numfashi ta COVID-19 a kasashen Afirka ya ragu, don haka ana iya cewa, kasashen nahiyar sun samu sakamako wajen yaki da cutar.
Alkaluman da cibiyar dakilewa da kuma rigakafin cututtuka ta Afirka CDC ta fitar a ranar 20 ga wata sun nuna cewa, kawo yanzu gaba daya adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a kasashen Afirka ya kai sama da miliyan 1 da dubu 660, kuma kusan dubu 40 dake cikinsu sun rasu sakamakon cutar, kana mutanen da yawansu ya kai miliyan 1 da dubu 360 sun warke daga cutar. Jami'ar hukumar kiwon lafiya ta duniya dake kula da harkokin lafiya a Afirka, Matshidiso Rebecca Moeti ta bayyana cewa, tun bayan barkewar annobar, adadin mutanen da suka kamu da cutar bai karu da babban mamaki ba.
An lura cewa, dalilin haka shi ne, domin kasashen Afirka suna mai da hankali kan aikin tantance kwayar cutar, kuma suna kokari matuka domin shawo kan annobar cikin hanzari.
A watan Fabrairun bana, an kafa dakunan tantance kwayar cutar biyu kacal a kasashen Afirka ta Kudu da kuma Senegal, amma yanzu adadin dakunan gwajin da aka kafa a nahiyar ya riga ya kai fiye da 750, kuma bisa kididdigar da ofishin hukumar kiwon lafiya ta duniya dake Afirka ya yi, dakunan gwaji 12 da aka kafa a kasashen Afirka sun riga sun kai ma'aunin gwaji na hukumar, kuma kawo yanzu, adadin mutanen da aka yi wa gwaji ya zarta miliyan 15.
Kuma gadajen asibitocin da suke jiyyar masu kamuwa da cutar a kasashen Afirka sun karu daga dubu 13 a watan Afililun bana zuwa dubu 43 a watan Agusta, ma'aikatan kiwon lafiya da yawansu ya kai dubu 150 sun samu horon da hukumar kiwon lafiya ta duniya da kungiyoyin da abin ya shafa suka samar, kana ma'aikatan kiwon lafiya dake aiki a asibitocin unguwannin kasashen sama da dubu 340 suna kokarin yada ilmin kandagarkin cutar bayan horon da aka yi musu. Ban da haka, kayayyakin kiwon lafiya da kasashe da kungiyoyin kasa da kasa suka samarwa kasashen Afirka sun kai miliyan 48.
Babban darektan hukumar kiwon lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa, kasashen Afirka da yawan gaske sun taba yaki da cututtuka masu yaduwa daban daban, lamarin da ya kai su ga samun fasahohi da dama da suka taimake su yayin da suke kokarin dakile annobar COVID-19. Misali, tun farkon barkewar cutar, nan take yawancin kasashen Afirka suka dauki matakan kulle, wasu kuma sun dauki matakin ne tun kafin a samu bullar cutar a kasashensu.
Hakika tun daga watan Maris din bana, masanan kandagarkin cututtuka na kasar Sin sun shirya taron musayar fasahohin dakile cutar ta kafar bidiyo sau da dama da ma'aikatan kiwon lafiya na kasashen Afirka da dama, inda daruruwan jami'an kiwon lafiya da suka fito daga kasashen Afirka sama da 40 da kungiyar tarayyar Afirka wato AU suka tattauna da masanan kasar Sin domin kandagarkin cutar tare. Kana kawo yanzu gaba daya kayayyakin kiwon lafiya da gwamnatin kasar Sin ta samar wa kasashen Afirka 53 da kungiyar AU sun kai tan 400, kuma ta samar da gatanci ga kasashen Afirka domin su sayi kayayyakin kandagarki daga wajenta, ban da haka, kasar Sin ta tura tawagoyin masana kiwon lafiya ga kasashen Afirka sama da goma, har asibitoci 46 na kasashen Afirka 42 sun tabbatar da cewa, za su gudanar da hadin gwiwa tsakaninsu da takwarorinsu na kasar Sin.
Darektan cibiyar dakilewa da kuma rigakafin cututtuka ta Afirka CDC John Nkengasong ya jinjinawa tallafin da kasashen duniya musamman kasar Sin suke samarwa kasashen Afirka matuka, yana ganin cewa, a karkashin jagorancin kungiyar AU da cibiyar CDC Afirka, kasashen Afirka sun dauki matakin dakile annobar tare cikin hanzari, sun kuma kafa dandalin sayen kayayyakin kiwon lafiyar da suke bukata cikin hadin gwiwa, da haka gwamnatocin kasashen Afirka suka iya samun kayayyakin kiwon lafiya cikin lokaci, haka kuma suna iya gudanar da aikin dakile annobar lami lafiya.
Haka zalika, hukumar kiwon lafiya ta duniya ta yi kira ga kasashen Afirka da su ci gaba da kara tsauraren matakan kandagarkin cutar, tare kuma da aiwatar da manufar da ta dace da kiyaye lafiyar jama'a, ta yadda za su hana sake barkewar cutar.(Jamila)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China