Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda Sweden Ta Ci Zalin Kamfanonin Kasar Sin Zai Illanta Moriyar Kanta
2020-10-21 21:26:49        cri

Kwanan baya, hukumar sa ido kan harkokin aikin sadarwa ta kasar Sweden ta sanar da cewa, batun tsaro ne ya sa kasar ta haramtawa kamfanin Huawei, da kamfanin ZTE na kasar Sin, su shiga ayyukan raya tsarin fasahar 5G a kasar. Ta kuma bukaci kamfanin ZTE da ya rushe dukkan na'urorin da ya riga ya ajiye a kasar, kafin ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2025.

Sanin kowa ne cewa, Sweden ta bi sahun kasar Amurka ne, wajen cin zalin kamfanonin kasar Sin da sunan siyasa. Kaza lika Sweden ta dauki matakin ne bisa hujjar tsaro, duk da cewa ba ta da wata shaida game da hakan.

To amma ko me ya sa Sweden ta ci zalin kamfanonin kasar Sin? Dalilin ba ya wuce tasirin wasu 'yan adawar kasar Sin dake kasar, haka kuma wasu tsirarun 'yan siyasan Amurka sun ba da nasu tasirin a Sweden. Ban da haka kuma, wani dalili na daban da ya sa Sweden ta haramtawa kamfanonin kasar Sin ayyukansu, shi ne cin zalin 'yan takarar kamfanonin Sweden, a kokarin taimaka musu kara samun rabon kasuwa.

To amma hakan ya dace da bude kofa ga ketare da kuma yin hadin gwiwar moriyar juna? Ko kuma dai mataki ne na zama 'yar tsana a hannun Amurka? Ga alama Sweden ba ta yi tunani sosai kan zabin da ta yi ba. Domin kuwa hakan zai illanta moriyar kanta. Ya fi kyau Sweden ta mutunta ka'idojin kasuwa na bude kofa ga kowa, da yin adalci a tsakanin kowa da kowa, ta kai zuciya nesa, ta yi tunani kan lamarin, ta gyara kuskurenta cikin hanzari. Idan kuwa Sweden ta yi gaban kan ta, ta ci gaba da zama 'yar tsana a hannun Amurka, matakin zai haifar mata da mummunan sakamako. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China