Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana gudanar da aikin nazarin allurar rigakafin COVID-19 lami lafiya a kasar Sin
2020-10-21 11:08:44        cri

Jiya Talata majalisar gudanarwar kasar Sin ta shirya taron manema labarai kan aikin rigakafi da dakile annobar cutar numfashi ta COVID-19 a nan birnin Beijing, inda aka bayyana cewa, a halin yanzu ana gudanar da aikin nazarin allurar rigakafin cutar lami lafiya a kasar ta Sin, har ya kai sahun gaba a fadin duniya, kuma kasar Sin za ta ci gaba da yin kokari tare da sauran kasashe domin kiyaye tsaron rayukan al'ummun duniya.

Yayin taron manema labarai kan aikin rigakafi da kuma dakile annobar cutar numfashi ta COVID-19 da majalisar gudanarwar kasar Sin ta kira a jiya Talata, mataimakin shugaban hukumar kimiyya da fasahar raya zaman takewar al'umma ta ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Tian Baoguo ya bayyana cewa, kawo yanzu jimillar allurar rigakafin cutar COVID-19 da ake yin gwaje kan mutane ta kai 13, yana mai cewa, "A halin da ake ciki yanzu, aikin nazarin allurar rigakafin COVID-19 na kasar Sin yana sahun gaba a fadin duniya, an shiga mataki na uku na gwajin allurar guda hudu da ake a kan mutane lami lafiya, kuma ga alamu, alluran ba su wata illa ga lafiya"

Yayin taron, shugaban rukunin SINOPHARM wato rukunin maganin kasar Sin Liu Jingzhen ya bayyana cewa, "Yanzu ana yin gwajin allurar rigakafin cutar COVID-19 guda biyu da cibiyar nazarin halittu ta birnin Beijing da takwarar ta dake birnin Wuhan a mutane a kasashe goma da suka hada da Hadaddiyar Daular Larabawa da Jordan da Peru da Agentina da Masar da sauransu bisa mataki na uku, kawo yanzu jimillar mutanen da aka yiwa allurar ta kai wajen dubu 50, gaba daya za ta kai sama da dubu 60, mutanen da aka yiwa allurar sun zo ne daga kasashe 125, ana iya cewa, aikin nazarin allurar da ake gudanarwa a kasar Sin ya kai sahun gaba a duniya, a don haka ya samu amincewa daga duk fannoni a duniya."

Liu Jingzhen shi ma ya fayyace cewa, a shirye rukuninsa yake wajen samar da allurar masu yawan gaske, an yi hasashen cewa, a cikin shekara mai zuwa, jimillar allurar da rukunin zai samar za ta kai biliyan 1, jimillar da za ta biya bukatun kasar matuka.

Kawo yanzu kasar Sin ta riga ta shiga shirin samar da allurar rigakafin COVID-19 wato COVAX da hukumar kiwon lafiya ta duniya da kungiyar samar da allurar rigakafin cututtuka ta kasa da kasa suka tsara. Kan wannan batun, jami'in hukumar kasa da kasa ta ma'aikatar harkokin wajen kasar Zhao Xing ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi alkawari cewa, bayan da ta kammala aikin nazarin allurar rigakafin COVID-19, ta kuma fara samar da kuma amfani da allurar, za ta samar da su ga al'ummar duniya, kana kasashe masu tasowa za su fara amfani da su, yana mai cewa, "Har kullum gwamnatin kasar Sin tana nacewa kan manufar gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, domin ganin bayan annobar, yanzu haka gwamnatin kasar tana sa kaimi kan aikin nazarin allurar rigakafin cutar, domin yin nasarar samar da allurar cikin hanzari, ta yadda za a samar da allurar ga kasashe masu tasowa, dalilin da ya sa haka shi ne, kasar Sin tana sauke nauyin harkokin kasa da kasa da matsayinta na babbar kasa a duniya, tare kuma da ciyar da aikin gina kyakkyawar makomar kiwon lafiya ta bil Adama gaba yadda ya kamata, nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da yin kokari tare da sauran kasashe domin tabbatar da tsaron rayukan al'ummun duniya."(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China