Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Taron ministoci ya samar da dala biliyan 1.7 don gudanar da ayyukan jin kan bil adama a tsakiyar yankin Sahel
2020-10-21 10:44:21        cri

A ranar Talata masu bayar da taimako sun yi alkawarin samar da kudade sama da dala biliyan 1.7 a lokacin taron ministoci domin inganta shirin ceton rayukan bil adama a yankin tsakiyar Sahel, wanda ya kunshi kasashen Burkina Faso, Mali da Nijer, masu shirya taron ne suka sanar da hakan.

Gudunmawa mafi girma ta fito ne daga kasar Switzerland inda ta yi alkawarin bayar da dala miliyan 464.1 nan da shekaru biyu masu zuwa, sai Amurka wacce ta yi alkawarin dala miliyan 274.8, yayin da kasar Denmark ta alkawarta bayar da dala miliyan 183.1, sai kungiyar tarayar turai EU za ta bayar da dala miliyan 122.8, sai kuma Jamus za ta bayar da tallafin dala miliyan 118.2, kamar yadda alkaluman da MDD ta sanar, a taron da aka gudanar ta kafar bidiyo tsakanin kasashen Denmark, Jamus, da EU.

Tashe-tashen hankula ya yi sanadiyyar raba mutane sama da miliyan 1.5 da gidajensu a tsakiyar yankin Sahel, wanda ya ninka sau ashirin a cikin shekaru biyu. Ayyukan cin zarafi ya yi matukar karuwa a shiyyar, sannan miliyoyin yara ba su zuwa makaranta, ga kuma rashin ingantattun cibiyoyin kula da lafiya da karancin tsarin kyautata rayuwar al'umma. Adadin masu fama da karancin abinci ya karu inda ya ninka sau uku idan an kwatanta da shekara guda da ta gabata, a cewar sanarwar da masu shirya taron suka baiwa manema labaru.

A cewar babban sakataren MDD Antonio Guterres, yankin tsakiyar Sahel yana cikin halin rashin tabbas, kamar yadda ya bayyana a taron. Ya kara da cewa, ya kamata a gudanar da sauye sauye ta hanyar samar da matakan farfado da zaman lafiya da warware takaddama. Kana akwai bukatar a bullo da tsarin samar da muhimman taimakon jin kan bil adama da kuma zuba jari a fannin kyautata rayuwar al'umma.

Guterres ya bukaci a samar da tallafin dala biliyan 2.4 domin gudanar da ayyukan jin kan bil adama a ragowar watanni biyun shekarar 2020 da samar da tallafin gaggawa a cikin shekarar 2021. Gwamnatocin kasashe 24 da hukumomin bayar da tallafin sun amsa kiran jami'in MDDr.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China