Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An sake rufe makarantu a jihar Lagos saboda masu zanga-zanga
2020-10-20 11:23:26        cri
An sake rufe makarantu a jihar Lagos, cibiyar hada-hadar tattalin arziki ta Nijeriya, domin tabbatar da tsaron dalibai da makarantu da iyaye, yayin da zanga-zangar adawa da hallayar da ake zargin 'yan sanda da ita, ke kara kamari.

Wata sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar, ta ba makarantu shawarar amfani da wasu hanyoyin koyo da koyarwa daga nesa, ta hanyar amfani da rediyo da talabijin da kafar intanet, kamar dai yadda suke yi lokacin da aka sanya dokar kulle saboda cutar COVID-19.

A baya-bayan nan, zanga-zangar "EndSARS", wato adawa da rundunar 'yan sanda mai yaki da 'yan fashi da makami, na wakana a manyan biranen dake fadin Nijeriya, inda ake neman bin hakkin wadanda rundunar ta kashe ko ta ci zarafi.

Lagos ce kadai jihar da ta bada umarnin rufe makarantu saboda zanga-zangar. Inda gwamnatin jihar ta ce za ta sanar da lokacin bude su nan bada dadewa ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China