Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashe 184 sun shiga shirin COVAX
2020-10-20 10:22:17        cri

Jimilar kasashe 184 ne suka shiga shirin COVAX da hukumar lafiya ta duniya WHO da kawayenta ke jagoranta, domin tabbatar da al'ummar duniya sun samu riga kafin cutar COVID-19 yadda ya kamata kuma bisa adalci.

Yayin wani taro ta kafar bidiyo, darakta janar na hukumar WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesusu, ya ce shirin COVAX zai zama tamkar wani babban dandali na samar da riga kafin COVID-19, kuma hanya mafi dacewa ta tabbatar da an raba riga kafin cikin aminci da adalci a fadin duniya.

Ya kara da cewa, raba riga kafin cikin adalci ita ce hanya mafi sauri ta kare al'ummomin da suka fi fuskantar barazanar cutar da kuma farfado da tattalin arzikin duniya.

A matsayin daya daga cikin kasashen dake kan gaba wajen samar da riga kafin, kasar Sin ta shiga shirin a hukumance, yunkurin da kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta bayyana a matsayin mataki mai muhimmanci na daukaka manufar al'umma mai cike da lafiya ga kowa da kuma cika alkawarin kasar na samar da riga kafin ga dukkan sassan duniya.

Yayin da duniya ke kokarin dakile ci gaba da bazuwar cutar COVID-19, kasashe a fadin duniya na takarar neman riga kafin. A cewar shafin website na WHO, zuwa ranar 19 ga watan Oktoba, akwai nau'ikan riga kafi 198 da ake kokarin samarwa a duniya kuma tuni 44 daga cikinsu suka shiga matakin gwaji kan mutane. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China