Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Karuwar Wasu Alkaluma Sun Bayyana Farfadowar Tattalin Arzikin Kasar Sin Ba Tare Da Wata Matsala Ba
2020-10-19 19:55:54        cri
Yayin da ake ci gaba da fama da annobar cutar numfashi ta COVID-19 a wasu sassan duniya, kasar Sin ta sake nuna wa duniya cewa, abu ne mai yiwuwa, a samu saurin farfadowar tattalin arziki, bayan da aka samu nasarar dakile yaduwar annobar, inda kasar ta Sin ta kaddamar da alkaluman tattalin arzikinta na watan Yuli zuwa Satumban bana a yau Litinin 19 ga wata. Hakan wani bangare ne na bayanin da jaridar "The New York Times" ta kasar Amurka ta wallafa.

Bayanin jaridar na kunshe da wasu alkaluman da hukumar harkokin kididdiga ta kasar Sin ta gabatar a yau, wadanda suka nuna saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya kai kaso 4.9 cikin 100 a watan Yuli zuwa Satumban bana. Kana kuma, karuwar GDP na watan Janairu zuwa Satumbar bana ta karu da kaso 0.7 cikin 100, bisa makamancin lokaci na shekarar bara. Kaza lika harkokin tattalin arzikin kasar Sin sun gudana ba tare da wata matsala ba.

Har ila yau, a karo na farko a bana, kudin shigar ko wane Basine, da kayayyakin bukatun yau da kullum da aka sayar a kasar Sin, da wasu alkaluman tattalin arzikin kasar Sin sun samu karuwa. Abin da ya kamata a lura da shi shi ne, manufofin kasar Sin na tabbatar da zaman rayuwar al'umma, da samar da guraben aikin yi suna aiki yadda ya kamata.

A cikin watan Janairu zuwa Satumban bana, an samar da guraben aikin yi miliyan 8 da dubu 980 a duk fadin kasar Sin, ta haka kasar Sin ta kusan cimma manufar da ta tsara a farkon wannan shekara.

Nan gaba kuma kasar Sin za ta ci gaba da dakile yaduwar annobar, tare da zurfafa yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare, za ta kara azama kan raya tattalin arzikinta yadda ya kamata, a kokarin cimma manufar raya kanta a bana. Kasar Sin za ta tabbatar da farfadowar tattalin arzikinta ba tare da wata matsala ba, za ta kuma ba da gudummawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya gwargwadon karfinta. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China