Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin Na Daukar Matakan Taimakawa Afirka Wajen Raya Aikin Gona
2020-10-19 15:32:28        cri

Ranar 16 ga watan Oktoba, ranar samar da abinci ce ta duniya, inda hukumar abinci da aikin gona ta MDD wato FAO ta kebe "daukar matakan samun ci gaba mai dorewa, a kokarin raya kyakkyawar makoma" a matsayin babban takenta na bana. Haka kuma ranar 17 ga wata, rana ce ta kau da talauci ta duniya, inda MDD ta sanar da cewa, "daukar matakai tare, don yiwa kowa adalci a cikin al'umma" shi ne babban taken ranar bana.

Duk wadannan ranakun biyu na dora muhummanci kan aikin daukar mataki don yaki da yunwa da fatara. Sakamakon bullar cutar COVID-19, batun samar da isasshen hatsi da aikin yaki da talauci na fuskantar kalubale mai tsanani a Afirka. A matsayinta ta aminiyar Afirka a ko da yaushe, kasar Sin na daukar matakan a zo a gani domin taimakawa Afirka wajen ci gaban aikin gona, da kyautata yanayin tsaron abinci, da ma bunkasar aikin yaki da talauci.

Yunwa da fatara matsaloli ne da suka dade suna damun nahiyar Afirka a kokarinta na samun ci gaba. Alkaluman kididdigar da MDD ta fitar na nuna cewa, akwai 'yan Afirka kimanin miliyan 250 dake fama da yunwa. Abin da ya fi kamari shi ne, adadin ka iya karuwa sakamakon tabarbarewar tattalin arzikin Afirka a shekarar da muke ciki, bayan bullar cutar COVID-19.

Tun shekaru da dama da suka gabata, kasar Sin ta fara tura kungiyoyin kwararru a fannin ayyukan gona zuwa kasashen Afirka, sa'an nan ta kafa cibiyoyin gwajin ayyukan gona na zamani a kasashen domin koyar da manoma da ma'aikatan da abin ya shafa na wurin fasahohin tafiyar da harkokin kula da ayyukan gona, ta yadda za a kyautata aikin gona. Ban da wannan kuma kasar Sin ta horar da kwararrun Afirka a wannan fanni, da ma shirya kwasa-kwasan horar da fasahohin noma a wurin.

Misali a cibiyar gwajin fasahohin ayyukan gona ta Sin da Mozambique, kasar Sin ta taimaka wa Mozambique wajen samun sabbin irin shuka fiye da 80, wadanda suka shafi shimkafa, masara, auduga, wake, ridi da dai sauransu. Bugu da kari, an horar da manoma fiye da 3000 na wurin.

Shirin hadin kan aikin noma na Xai-xai na Sin da Afirka da ake gudanar da shi a birnin Xai-xai, hedkwatar jihar Gaza dake kasar Mozambique yana daga cikin hanyar shuke-shuke na hadin gwiwa don taimaka wa manoma wurin wajen raya gonaki da shuka shinkafa.

Joanna mai shekaru 55 da haihuwa wata manomiya ce da ta fara shiga shirin a shekarar 2015, ta furta cewa, shirin ya samar mata na'urorin aikin gona da irin shuka, sa'an an an koya mata yadda za ta daidaita filayen gonaki, kula da hatsi, da ma kau da kwari. Yayin da take magana kan yadda ta amfana da shirin, ta ce, kafin ta shiga shirin, tana shuka wake, masara a gonakin gidanta mai fadin kadada daya, amfanin gona ya ishi iyalinta ne kawai. Amma bayan da ta shiga shirin, ta samu riba sosai. Tana iya biyawa jikanta kudin makaranta, da ma sayen abinci da tufafi na gari, har ma ta sayi firiji da murhu mai amfani da iskar gas. Dukkan wadannan abubuwa ba ta yi zato za ta same su a da ba, a cewarta.

A nasa bangaren, Christopher Kapembwa, kwararre a cibiyar nazarin ayyukan gona ta Zambiya ya bayyana cewa, suna maraba da karin Sinawa masu zuba jari zuwa kasarsa wajen raya ayyukan gona, lamarin da ba ma kawai zai taimaka wajen karuwar yawan amfanin gona da kasashen Afirke ke samarwa, da karuwar yawan kudin shiga da manoma ke samu ba, hatta ma zai sa kaimi ga karuwar yawan kudin shiga na wurin gaba daya.

Samun fasahohi daga shirye-shiryen hadin kan aikin gona da kasar Sin ta tsara domin samun sabuwar damar canja makoma da ma samun cigaba, shi ne burin dimbin 'yan Afirka a halin yanzu.

Emmanuel, dan kasar Ruwanda mai shekaru 34 da haihuwa, wani ma'aikacin gyaran na'urori ne a wata masana'antar samar da sukari. Ya fara aiki a kungiyar kwararrun Sin da ke kasarsa a shekarar 2008, inda ya koyi fasahar shuka laimar kwadi. Sakamakon fatansa ta samun kyakkyawar makomar aikin shuka laimar kwadi, Emmanuel ya kafa wani kamfanin samar da laimar kwadi a shekarar 2016 da kudin da ya ajiye.

Shugaban kwamitin kula da ayyukan gona na kasar Ruwanda Patrick Karangwa ya yi nuni da cewa, jama'a na karuwa a kasar, kuma laimar kwadin da aka ci da amfani da su a matsayin magunguna, wani nau' in amfanin gona ne da zai samar da babbar riba. Ana sa ran aikin shuka laimar kwadi zai taka muhimmiyar rawa a aikin canja salon raya ayyukan gona na Ruwanda, baya ga kyautata yanayin al'umma na samun amfanin gina jiki.

Shekaru hudu bayan da Emmanuel ya bude kamfaninsa, yanzu kamfanin yana samar da laimar kwadi na buhuna kimanin dubu 10 a ko wane wata, yawan nauyin laimar kwadin da ya sayar ya zarce kilogiram 600 a ko wane wata. Ba ma kawai sun samu karbuwa a Ruwanba ba, har ma ana sayar da su a Jamhuriyar Demokuradiyyar Kongo da Uganda.

Tang Lixia, farfesa a jami'ar ilmin aikin gona ta kasar Sin ta bayyana cewa, abubuwan da aka tanada cikin hadin gwiwar Sin da Afirka ta fuskar ayyukan gona sun dace da Ajandar shekarar 2063 ta kungiyar tarayyar Afirka da shirin raya ayyukan gona na Afirka da sauran shirye-shiryen ci gaban Afirka, wadanda ke iya biyan bukatun Afirka da ma dacewa da muradun bangarorin biyu.

A nasa bangaren, Cavens Adhir, masanin ilmin dangantakar kasa da kasa na kasar Kenya ya furta cewa, ya zuwa karshen shekarar 2020, Sin za ta cimma nasarar yaki da kangin talauci, ta hakan za ta warware matsalar fama da talauci da ke damunta har na tsawon shekaru fiye da 1000. Duk da kalubale da ake fuskanta sakamakon bullar cutar COVID-19, kasar Sin za ta cimma wannan babban buri. Haka kuma ta hanyar koyon fasahohi daga kasar Sin, dimbin kasashen Afirka na kokarin yaki da talauci, wadanda suka riga suka samu wasu sakamako na a zo a gani.(Kande Gao, sashen hausa na CRI)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China