Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Iran tace an dage takunkumin MDD da aka kakaba mata
2020-10-19 10:41:19        cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta sanar cewa, takunkumin hana cinikin makamai da MDD ta kakaba mata ya zo karshe a ranar Lahadi a hukumance bisa ga tsarin yarjejeniyar nukiliyar Iran ta shekarar 2015.

A wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ta ce, daga yanzu, dukkan takunkuman cinikin makamai, da sauran harkokin dake shafar mu'amalar kudade da kasar ta Iran sun zo karshe.

Sanarwar tace, babu sauran wani mataki na musamman daga bangaren Iran a yayin da takunkumin ya zo karshe matukar kwamitin sulhun MDD bai sake tsawaita wa'adin ba.

Bugu da kari, sanarwar tace, Iran ta dogara ne da kanta ta fuskar tsaron kanta saboda bata da sukunin sayen makamai.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China