Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnonin jihohin Amurka sun nemi gwamnatin tarayya ta yi musu Karin haske game da shirin riga kafin COVID-19
2020-10-19 09:42:14        cri
A jiya ne kungiyar gwamnonin jihohin Amurka (NGA) ta aikewa gwamnatin Trump jerin tambayoyi, inda take neman Karin haske kan yadda gwamnatin tarayya za ta raba da ma yi wa 'yan kasar allurar riga kafin COVID-19.

Da yake jawabi yayin taron manema labarai, shugaban kungiyar gwamnonin, gwamnan jihar New York Andrew Cuomo ya bayyana cewa, jerin tambayoyin da gwamnonin jam'iyyun Republican da Democrat daga sassan kasar suka gabatar, sun shafi batun kudaden da za a kashe wajen yi wa 'yan kasar riga kafi, da tsarin rabawa da samar da riga kafin, da ka'idojin tattaunawa da muhimman bayanai.

An ruwaito gwamna Cuomo na cewa, wajibi ne a fito da managarcin tsarin rabawa da yadda za a aiwatar da riga kafin, da taimakon kudi tsakanin gwamnatocin jihohi da na tarayyar kasar.

A jiya ne, shugaba Donald Trump na Amurkar, ya bayyana cewa, Amurka za ta samar da isassun alluran riga kafin cutar COVID-19 ga daukacin Amurkawa, nan da watan Afrilun shekarar 2021.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China