Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana bukatar jurewa wajen fama da kangin talauci
2020-10-18 20:18:10        cri

A shekarar 1980, bisa ma'aunin fama da talauci da MDD ta fitar, ya nuna duk mutumin da ba zai iya samun dala 1.9 a duk rana ba, to shi ne mutum mai fama da kangin talauci. Yawan mutanen dake fama da kangin talauci a nan kasar Sin ya kai kashi 88.3 cikin dari bisa jimillar yawan mutanen duk kasar Sin. A wancan lokaci, yawan Sinawa ya kai biliyan 1, sakamakon haka, yawan mutanen da suke fama da kangin talauci ya kai kusan miliyan 900. Amma bisa shirin da gwamnatin kasar Sin ta fitar, kawo karshen bana, kasar Sin za ta fitar da dukkan mutane da kananan hukumomi masu fama da kangin talauci daga yanayin kuncin rayuwa. Mutane da yawa suna tambayar shin ta yaya kasar Sin ta samu wannan nasara cikin shekaru 40 kadai? A ganina, dalili mafi muhimmanci da ya sanya kasar Si ta samu wannan nasara shi ne, gwamnati da al'ummun kasar Sin ba su taba dakatar da gwagwarmayar yaki da kangin talauci cikin wadannan shekarun na baya ba. Sun kuma fitar da manufofi da matakai daban daban masu tarin yawa domin tabbatar da cimma wannan buri.

Da farko dai, gwamnatin kasar Sin ta tsai da kudurin aiwatar da manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofarta ga ketare a karshen shekarar 1978, domin hanzarta bunkasa tattalin arzikin kasar, da kuma kyautata zaman rayuwar al'umma. Sanin kowa ne, kawo yanzu kasar Sin ta riga ta yi shekaru 40 tana aiwatar da wannan manufa, ta kuma cimma burinta na bunkasa tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar al'umma.

Sannan, bisa wannan babbar manufa, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai daban daban wadanda suke daidai da hakikanin yanayin da ake ciki a lokuta daban daban da yankuna daban daban wajen fama da kangin talauci. Alal misali, a shekarar 1984, gwamnatin kasar Sin ta fitar da "Sanarwar hanzarta taimakawa wasu yankuna wajen sauya yanayin fama da kangin talauci", bayan an samu wasu ci gaba a wadannan yankuna, ta kuma fitar da wata sanarwa daban a shekarar 1987, wato "Sanarwar karfafa bunkasa tattalin arziki a yankuna masu fama da kangin talauci". Sannan a shekarar 1990, ta fitar da "Sanarwar kara karfafa gwagwarmayar yaki da talauci a shekarun 1990". Bugu da kari a shekarar 1994, gwamnatin kasar Sin ta fitar da "babban shirin kawar da kangin talauci a lokacin da ake aiwatar da 'shirin bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma na shekaru biyar-biyar na 8". Dadin dadawa, a shekarar 1996, kwamitin kolin JKS da gwamnatin kasar Sin sun tsai da "kudurin daidaita matsalar rashin abinci da masu fama da kangin talauci a kauyuka suke fuskanta".

A hakika dai, wadannan takardun da na ba ku wasu kalilan ne kawai daga cikin dukkan manufofi da matakan yaki da kangin talauci da kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS da gwamnatin kasar suka dauka a cikin shekaru fiye da 40 da suka gabata.

Ban da manfofi da matakan da gwamnatin kasar Sin suka dauka, hukumomi da gwamnatoci a matakai daban daban na kasar Sin sun kuma dauki matakan gwaji daban daban domin neman samun dabaru masu dacewa wajen fama da kangin talauci a yankuna daban daban. Alal misali, yankin Bijie dake arewa maso yammacin lardin Guizhou, inda aka yi gwagwarmayar yaki da kangin talauci matuka. A farkon shekarun 1980, a cikin mutane miliyan 5.6 na yankin, miliyan 3.12 suna fama da kangin talauci, yawan kudin shiga da kowane mutumin yankin Bijie ya samu ya kai kudin Sin yuan 184, kwatankwacin dalar Amurka 90 kawai, tare da yawan hatsin da kowa ke samu bai kai kilogram 200 ba a duk shekara. A cikin wasu magidanta, mutane hudu suna da kwano uku kawai. Har ma a wasu yankuna, wasu mutane ba su iya fitowa daga gida ba sakamakon rashin tufafi. To shin ko ta yaya za a iya daidaita matsalar? Bisa binciken da aka gudanar ya nuna cewa, kasar Sin ta mayar da yankin Bijie ya zama yankin gwajin dabarun kawar da talauci na farko a duk fadin kasar. Bisa manufofin musamman da gwamnatin tsakiya da ta lardin Guizhou suka bayar, da taimako daga sassa daban daban na kasar, da kuma kokarin al'ummun yankin, yanzu an kawar da kangin talauci gaba daya daga yankin.

Bugu da kari, kokarin da al'ummun Sinawa suka yi ba tare da kasala ba cikin wadannan shekaru 40 da suka gabata. Alal misali, bayan gwamnatin kasar Sin ta mayar da yankin Bijie ya zama yankin gwajin dabarun yaki da kangin talauci na farko a duk fadin kasar Sin, al'ummun yankin sun yi kokarin neman dabarun kawar da kangin talauci ba dare ba rana. A yankin, akwai wata jimla da ke shaida yadda ake kokari, wato "mun kaddamar da aikinmu kafin wayewar gari, amma mun koma gida bayan faduwar rana." Yankin Bijie, wuri ne dake cikin duwatsu, inda babu isassun gonakin noma da shuke-shuke. Sabo da haka, al'ummun yankin sun tsaida kudurin dashen bishiyoyi domin kare muhalli, sannan ana noman dankalin Turawa da raya sana'ar yawon bude ido domin samun karin kudin shiga.

Sabo da haka, ina ganin cewa, dalillin da ya sa kasar Sin ta cimma nasarar kawar da kangin talauci a duk fadin kasar ba domin ta maida hankali kan gwagwarmayar a cikin wadannan shekarun baya kawai ba ne, a cikin dimbin shekarun da suka gabata bayan kafuwar Jamhuriyar Al'ummar kasar Sin, kwamitin kolin JKS da gwamnatin tsakiyar kasar, har ma al'ummun kasar, da ma kungiyoyi masu zaman kansu ba su taba dakatar da neman dabaru masu dacewa na gwagwarmayar yaki da talauci ba. Bayan shekarar da muke ciki, wato bayan ta cimma nasarar kawar da kangin talauci daga kasar gaba daya a karshen shekarar, za su kuma ci gaba da yin kokarin kara kyautata zaman rayuwar al'umma domin biyan bukatun neman samun zaman rayuwa mai armashi da al'ummun kasar suke da su. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China