Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'ai: kasar Sin tana taka rawar gani a kokarin tabbatar da tsaron abinci a duniya
2020-10-18 16:58:51        cri
Wasu jami'ai na kasar Sin da na MDD sun ce kasar Sin ta riga ta zama wani bangaren dake taka rawar a-zo-a-gani, a kokarin tabbatar da tsaron abinci a duniya. Sun bayyana haka ne a ranar abinci ta duniya, wadda ta kasance ranar Juma'ar da ta gabata a wannan shekarar da muke ciki.

Yayin da ake fuskantar cutar COVID-19, gwamnatin kasar Sin ta dauki dimbin matakai don tabbatar da samar da isasshen abinci a kasar, a sa'i guda kuma, matakan sun taimaka wajen takaita hauhawar farashin abinci a kasuwanni, in ji Marielza Oliveira, mai rikon mukamin wakiliyar hukumar kula da abinci da aikin gona ta MDD dake nan kasar Sin.

Madam Oliveira, ta kara da cewa, kamfanonin kasar Sin masu sayar da kayayyaki ta shafin Intatet su ma sun dauki sabbin fasahohi don neman sayar da karin kayayyakin amfanin gona ta shafin Intanet.

A nasa bangare, Zhang Wufeng, shugaban hukumar kula da abinci da sauran kayayyaki masu muhimmanci da ake ajiyarsu ta kasar Sin, ya ce, kasar Sin ta samar da babbar gudunmawa ne, ta hanyar yin amfani da gonaki da fadinsu ya kai kashi 9 bisa 100 na duk duniya, da kashi 6 % na albarukatun ruwa na duniya, wajen biyan bukatun kashi 20% na al'ummar duniya wajen samun abinci. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China