Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Guterres ya yi kira a samar da abinci mai dorewa ga daukacin al'ummun kasa da kasa
2020-10-17 16:29:02        cri

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya gabatar da wani rahoto domin taya murnar ranar abinci ta duniya, inda ya bayyana cewa, ya zama wajibi a yi kokarin samar da abinci mai dorewa ga daukacin al'ummun kasashen duniya, haka kuma a rage abincin da ake batawa.

Guterres ya kara da cewa, annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta tsananta matsalar karancin abinci a duniya da ba a taba ganin irinsa ba cikin shekaru gomai da suka gabata. Ya ce yanzu adadin mutanen da suke fama da karancin abinci a fadin duniya ya kai miliyan 690, kuma ya zuwa karshen bana, kila adadin ya karu da mutane kusan miliyan 130, a sa'i daya kuma, mutane sama da biliyan 3 ba su da isasshen kudin sayen abinci mai inganci.

Babban jami'in ya ci gaba da cewa, yayin da ake murnar cika shekaru 75 da kafa hukumar samar da abinci da kula da aikin gona ta MDD, ya dace a kara kokarin cimma muradun samun ci gaba masu dorewa, wanda zai tabbatar da cewa, nan gaba daukacin al'ummun kasashen duniya za su samu abinci mai gina jiki a ko ina.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China