Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mene ne dalilin da ya sa aka yaba da fasahohin yaki da talauci na kasar Sin
2020-10-17 15:44:06        cri

Yau Asabar, 17 ga watan Oktoba, rana ce ta yaki da talauci ta kasar Sin ce, haka kuma ranar kawar da talauci ta duniya. Alkaluman da bankin duniya ya fitar sun nuna cewa, ma'aunin talauci na duniya na nufin ko wanen mutum ya kashe dala 1.9 a ko wace rana, wato wanda ya gaza kashe adadin, na fama da talauci, kasar Sin ta riga ta kubutar da al'ummunta da yawansu ya kai sama da miliyan 800 daga kangin talauci a cikin shekaru 40 da suka gabata, wato tun bayan da aka fara aiwatar da manufar bude kofa ga ketare da yin kwaskwarima a cikin gida a kasar ta Sin, adadin da ya kai kaso fiye da 70 bisa dari bisa na daukacin mutanen da suka fita daga kangin talauci a fadin duniya a cikin wadannan shekaru 40. Kana daga shekarar 2012 zuwa karshen shekarar 2019, kason talaucin kasar Sin ya ragu daga 10.2 bisa dari zuwa 0.6 bisa dari. Abun farin ciki shi ne, bayan kasar Sin ta cimma burin kawar da talauci daga duk fannoni a fadin kasar nan da karshen shekarar da ake ciki, za ta cimma muradun samun ci gaba mai dorewa na MDD nan da shekarar 2030 kafin shekaru goma da aka tsara, lamarin da zai taka rawar gani ga aikin yaki da talauci na kasashen duniya.

To mene ne dalilin da ya sa kasar Sin ta samu sakamako a wannan fannin? Yayin dandalin taron kolin tattaunawa kan yaki da talauci da samun ci gaba da aka shirya a shekarar 2015, shugaban kasar Sin ya taba bayyana cewa, "Mun nace ga manufar yaki da talauci ba tare da rufa rufa ba, kuma muna kokarin kawar da talauci ta hanyar raya tattalin arzikin kasarmu."

Kana kasar Sin tana himma da kwazo kan hadin gwiwar dake tsakaninta da sauran kasashe masu tasowa yayin da take kokarin yaki da talauci a cikin kasar, haka kuma tana samar da tallafi ga kasashe masu tasowa, musamman ga kasashen dake fama da talauci, misali ta gabatar da shawarar kafa sabon bankin raya kasashen BRICS wato NDB da bankin AIIB, kuma ta gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya domin samun ci gaba tare da kasashen da suka shiga shawarar, duk wadannan sun samar da muhalli mai inganci ga kasashe masu tasowa yayin da suke yaki da talauci.

Ban da haka, MDD ta yi hasashen cewa, akwai matukar wahala a cimma burin kawar da talauci bisa muradun samun ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2030 sakamakon yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19, a don haka fasahohin da kasar Sin ta samu a fannin za su taka rawa a bangaren, nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da hada hannu da sauran kasashen duniya domin farfado da tattalin arzikin duniya, tare kuma gabatar da dabarunta yayin da ake yaki da talauci a fadin duniya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China