Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan siyasar Amurka suna neman mayar da kasarsu saniyar ware
2020-10-16 20:20:16        cri

Jaridar Yomiuri Shimbun ta kasar Japan ta bayar da rahoto yau cewa, wasu jami'an gwamnatin kasar sun fayyace cewa, kasar ta Japan ta riga ta sanar da gwamnatin Amurka cewa, ba za ta shiga shirinta na mayar da kamfanonin kasar Sin gyefe guda a bangaren tsarin sadarwa ba, yunkurin 'yan siyasar Amurka na samun moriya ta hanyar yin barazana ga kawayen kasarsu ya gamu da rashin nasara, lamarin ya nuna cewa, amfani da harkokin diplomasiya wajen kai barazana ba zai yi tasiri a zamanin da cudanyar kasa da kasa ke kara samun karbuwa ba.

Abun mamaki shi ne, wasu 'yan siyasar Amurka sun zargi kasar Sin cewa, tana kawo barazana ga sauran kasashen duniya, makarkashiyarsu ita ce, lalata huldar dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashe, tare kuma da matsa musu lambar yin zabin ko dai su goyi bayan kasar Sin ko Amurka, amma hakika al'ummun kasashen duniya sun riga sun gano wace ce ke kawo barazana ga duniya, ko kuma wace ce ke lalata kwanciyar hankalin duniya.

Abun faranta rai shi ne, yawancin kasashen duniya sun yi zabin da ya dace, babban wakilin kungiyar tarayyar Turai wato EU kan harkokin harkokin diplomasiya da tsaro Jose Borrell ya bayyana cewa, duk da cewa, kungiyar EU tana fuskantar matsin lamba daga babbar kasa, amma ba za ta yi adawa da kasar Sin tare da Amurka ba. Ministan harkokin wajen kasar Austria Alexander Schallenberg shi ma ya nuna cewa, kasarsa ba za ta aiwatar da manufar hana ko kayyade harkokin wani kamfani ba, a maimakon haka tana kokarin bullo da wani tsarin bayanai mai inganci. A bayyane an lura cewa, yawancin kasashen duniya sun fahimci yunkurin wadannan 'yan siyasar Amurka sosai.

Kana Amurka ita ma tana kawo barazana ga wasu kungiyoyin kasa da kasa, misali tun bayan barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, Amurka ta sha yi wa hukumar kiwon lafiya ta duniya barazana, inda ta bukace ta da ta gyara tsarinta, har ma ta yi kashedi cewa, za ta fice daga hukumar, kuma kila za ta kafa wata hukuma ta daban domin maye gurbin hukumar kiwon lafiya ta duniya, duk wadannan sun lalata hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa yayin da suke kokarin dakile annobar tare. Kamar yadda wasu masu nazarin harkokin yau da kullum suka bayyana, 'yan siyasar Amurka wadanda ke aiwatar manufar diplomasiya ta hanyar kawo barazana sun riga sun kasance daliban da suka lalata tsarin kasa da kasa da ka'idar cudanyar bangarori daban daban.

Hakika kasashen duniya da dama sun riga sun fahimta cewa, sabanin dake tsakanin kasar Sin da Amurka ba takarar mulki ko matsayin kasa a duniya ba ne, haka kuma ba sabani wajen tsarin zaman takewar al'umma ba ne, sabani ne tsakanin kiyaye adalci ko yada mugun tanani, kuma sabani ne tsakanin ra'ayin cudanyar bangarori daban daban ko bangaranci, a don haka, ya kamata daukacin kasashen duniya wadanda suke neman 'yancin diplomasiya da kuma nacewa kan adalci za su yi zabin da zai dace da yanayin da kasashensu ke ciki.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China