Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jimillar adadi na masu rasuwa saboda cutar COVID-19 a Amurka na iya kaiwa 240,000 nan da Nuwamba
2020-10-16 16:02:18        cri
Bisa hasashen nan da ranar 7 ga watan Nuwamba dake tafe, mai yiwuwa jimillar adadin masu rasa rayukansu, sakamakon harbuwa da cutar numfashi ta COVID-19 a Amurka, na iya kaiwa tsakanin mutum 229,000 zuwa 240,000.

Hasashen baya bayan nan na cibiyar kandagarki da hana yaduwar cututtuka ta Amurka, ya nuna cewa, adadin masu harbuwa da cutar a rana guda zai ci gaba da karuwa. Wasu alkaluma da cibiyar ta fitar a shafin ta na yanar gizo a ranar 14 ga watan nan, sun nuna cewa, sabon adadin da aka samu na masu harbuwa da cutar a rana guda ya kai mutum 59,761, wanda shi ne sabon adadi mafi yawa da aka samu tun bayan na ran 7 ga watan Agusta.

Alkaluman sun nuna cewa, a makon da ya gabata, matsakaicin adadin wadanda suke harbuwa da cutar a kasar ya kai mutum 50,000 a rana guda, yayin da matsakaicin adadin masu rasuwa ke kaiwa mutum 700.

Kaza lika jami'ar Johns Hopkins dake Amurkan, ta fitar da wasu alkaluma dake nuna cewa, ya zuwa yammacin jiya Alhamis agogon wurin, adadin masu dauke da cutar COVID-19 a kasar, ya dara mutum miliyan 7.97, ciki hadda mutane 217,000 da cutar ta hallaka. (SAMINU)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China