Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta samar da dala miliyan 10 don tallafawa masu fama da ambaliyar ruwa a Sudan ta kudu
2020-10-16 11:33:53        cri
Hukumar bayar da agaji ta MDD ta sanar da cewa, ta samar da dala miliyan 10 domin tallafawa rayuwar mutane 360,000 wadanda ambaliyar ruwa ta yi wa barna a Sudan ta kudu.

Alain Noudehou, jami'in hukumar agajin MDD a Sudan ta kudu, ya ce an samar da kudin ne karkashin babban asusun ayyukan gaggawa na MDD, CERF, domin taimakawa iyalai da ambaliyar ruwan ta tagayyara, domin saukaka musu wajen samun abinci, da wuraren zama na wucin gadi, da kuma ruwan sha mai tsafta.

Yace asusun na CERF ya samar da kudi dala miliyan 10 ne domin gudanar da ayyukan jin kai ta hanyar kafa asusun samar da tallafin ambaliyar ruwa na Sudan ta kudu.

Mutane 800,000 ne bala'in ambaliyar ruwan ya shafa a Sudan ta kudu tun daga watan Yulin wannan shekara, a cewar MDD.

Har yanzu akwai yankunan dake cikin ruwa wanda aka kiyasa ya tilastawa mutane kusan 368,000 ficewa daga muhallansu kuma sun gaza komawa gidajen nasu. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China