Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MINUSMA: An kashe jami'in wanzar da zaman lafiyar MDD a arewacin Mali
2020-10-16 11:03:20        cri
An kashe wani jami'in aikin wanzar da zaman lafiya na MDD da yammacin ranar Alhamis bayan da motar da yake ciki ta taka nakiyar ko ababen fashewa da aka binne a kusa da garin Kidal dake shiyyar arewa maso gabashin Mali, tawagar shirin wanzar da zaman lafiya ta MDD a Mali MINUSMA, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba.

MINUSMA ta ce, da misalin karfe 1:30 na rana, wata motar dakarun MINUSMA ta taka nakiya ko wasu ababen fashewa, kimanin kilomita 50 daga garin Kidal, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar jami'in kiyaye zaman lafiyar guda da kuma jikkata mutum guda.

Duk da cewa ba ta bayyana mutanen da lamarin ya rutsa da su ko 'yan wace kasa ba ne, amma MINUSMA, ta yi Allah wadai da babbar murya game da irin wadannan hare hare da ake kaiwa kan jami'an MDD, da 'yan kasar Mali, da kuma jami'an tsaron kasa da kasa, har ma da fararen hula wadanda ba su san hawa ba balle sauka.

A cewar Mahamat Saleh Annadif, wakilin musamman na babban sakataren MDD a kasar Mali, kana shugaban tawagar MINUSMA, ya ce ko kadan wadannan hare haren ba zasu tsorata jami'an tsaron MINUSMA ba, kuma a shirye suke su taimakawa mutanen kasar Mali da gwamnatin kasar a kokarinsu na maido da zaman lafiya mai dorewa a Mali.

Ya kuma jaddada cewa, hare haren da ake kaddamarwa kan jami'an wanzar da zaman lafiya na MDD tamkar aikata laifukan yaki ne a bisa dokokin kasa da kasa. (Ahamd)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China