Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bangarorin yankunan Hongkong da Macao sun yaba da gagarumin ci gaban da birnin Shenzhen ya samu cikin shekaru 40 da suka gabata
2020-10-15 13:50:01        cri

A jiya Laraba, a yayin gagarumin bikin murnar cika shekaru 40 da zaman Shenzhen yankin musamman na tattalin arziki, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabin da ya jawo hankulan nagartattun mutanen yankunan Hongkong da Macao, inda suka yaba da gagarumin ci gaban da birnin Shenzhen ya samu cikin shekaru 40 da suka gabata. Sannan suna ganin cewa, wannan muhimmin jawabi ya haskaka makomar bunkasa yankin Guangdong da Hongkong da Macao.

Mr. Henry Tang, mamban zaunannen kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta duk kasar Sin, kuma tsohon direktan hukumar kudi ta gwamnatin yankin musamman na Hongkong ya saurari muhimmin jawabin da shugaba Xi Jinping ya gabatar, ya fadawa wakilin CMG cewa, a cikin shekaru 40 da suka gabata, yankin Hongkong da birnin Shenzhen sun yi aiki tare, sun bayar da gagarumar gudummawa, har sun samu ci gaba tare a yayin da kasar Sin ta aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare ba tare da kasala ba. Mr. Henry Tang yana mai cewa, "Yau da safe, na saurari jawabin da shugaba Xi Jinping ya gabatar a yayin gagarumin bikin. Ni kaina na yi shekaru 40 ina samun ci gaba a birnin Shenzhen, wato na ga yadda Shenzhen, wani karamin kauye yau shekaru 40 da suka wuce, ya zama wani muhimmin birnin dake yiwa sauran sassan duniya tasiri. Ina iya fadi cewa, ni da birnin Shenzhen mun samu ci gaba tare. Sakamakon haka, yau ina farin ciki sosai da na saurari jawabin da shugaba Xi ya gabatar. Mun taba bayar da gudummawarmu wajen bunkasa birnin Shenzhen. Idan kowa ya bayar da gudummawarsa, za a iya samun karfin neman ci gaba na dukkan al'ummunmu Sinawa."

A lokacin da ya tunasar da lokacin kafa sashen kamfaninsa a birnin Shenzhen a farkon lokacin da kasar Sin ta kaddamar da manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga ketare, Henry Tang ya ce, an sha wahalhalu masu tarin yawa wajen bunkasa birnin Shenzhen.

"Mun kafa masana'antarmu ta farko a Shenzhen a shekarar 1978. A lokacin da aka kaddamar, masana'antar tana da benaye biyu ne kawai. Ofishina yana kan bene na biyu. Wani abin da ya burge ni sosai shi ne, hanyar dake hade masana'antarmu da sauran sassan birnin, wata hanyar tabo ce. Mun kafa wata masana'anta, tare da wasu dakunan kwana, mun samarwa ma'aikatanmu wurin kwana, da abinci, amma albashinsu bai kai kashi daya cikin shida na albashin ma'aikatan yankin Hongkong ba. Saboda haka, na san wahalhalun da aka sha domin bunkasa birnin Shenzhen da ya zama wani muhimmin birni mai kirkiro sabbin fasahohin zamani daga wani karamin kauye. Lalle an sha wahala da yawa."

Henry Tang ya kara da cewa, a lokacin da kasar Sin take samun ci gaba sakamakon kaddamar da manufofin yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga ketare, birnin Shenzhen da yankin Hongkong sun samu bunkasa tare. A nan gaba, yankin Hongkong zai iya bayar da karin gudummawa ga kasar Sin, ciki har da yankin Guangdong da Hongkong da Macao, da kuma birnin Shenzhen.

A bangaren nagartattun mutanen yankin Macao kuwa, sun bayyana cewa, a cikin jawabin da shugaba Xi Jinping ya gabatar, an tanadi fasahohi 10 da aka samu cikin shekaru 40 da suka gabata wajen bunkasa birnin Shenzhen. Mr. Pang Chuan, mataimakin shugaban jami'ar kimiyya da fasaha ta Macao yana mai cewa, "Manufofin yin gyare-gyare da bude kofa ga ketare da aka aiwatar sun jawo 'yan uwanmu na Macao da su koma babban yanki, ciki har da birnin Shenzhen domin neman bunkasuwa, har ma sun sanya mutanen Macao sun amince da kasarmu. Bunkasar birnin Shenzhen ya zama wani kyakkyawan tushe ga dawowar yankin Macao hannun kasar Sin."

Mr. Cui Shiping, shugaban kungiyar bunkasa kimiyya da fasaha ta Macao, kuma babban direktan cibiyar taimakawa matasa raya sana'o'insu ta Macao, ya bayyana cewa, "Abin da ya fi burge ni shi ne, shugaba Xi ya tanadi fasahohi 10 na bunkasa birnin Shenzhen, wasu daga cikinsu suna shafar yankunan Hongkong da Macao. Hakika, yadda za mu iya warware matsalolin da suke kawo mana cikas wajen kirkiro sabbin fasahohin neman ci gaba, ya zama wata babbar matsala, dole ne mu yi koyi da fasahohin da aka samu a birnin Shenzhen mu mayar da nasarar da Shenzhen ya samu ta zama abin koyi ga yankunan Hongkong da Macao." (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China