Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen duniya za su samu moriya daga ci gaban kasar Sin
2020-10-14 20:14:11        cri

Mujallar The Economist ta kasar Birtaniya ta taba bayyana cewa, "Abin al'ajabin Shenzhen ya kai sahun gaba a cikin yankunan tattalin arziki na musamman da yawansu ya kai sama da 4000 a fadin duniya."

Yayin babban taron murnar cika shekaru 40 da kafa yankin tattalin arziki na musamman na Shenzhen da aka shirya yau Laraba, shugaban kolin kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi, inda ya sanar da cewa, kasar Sin za ta kara bude kofa ga ketare, da kara zurfafa kwaskwarima a gida, da kuma raba moriyar ci gabanta ga sauran kasashen duniya, lamarin da zai kawo babban tasiri ga duk duniya.

Birnin Shenzhen ya shafe shekaru 40 kawai inda ya sauya daga wani karamin kauyen kama kifi zuwa babban birnin kasa da kasa, amma wasu manyan biranen ketare sun cimma burinsu ne bayan kokarin da suka yi cikin shekaru dari daya ko fiye. A shekarar 1980, adadin GDP na birnin ya kai kudin Sin yuan miliyan 270, amma ya karu zuwa yuan biliyan 2700 a shekarar 2019, adadin da ya karu da kaso 20.7 bisa dari a ko wace shekara, kana adadin kudin shiga na ko wane mutumin birnin ya kai yuan dubu 62.5 a shekarar 2019, adadin da ya ninka har sau 31.6 idan aka kwatanta da shekarar 1985, duk wadannnan sun nuna cewa, matakin kafa yankin tattalin arziki na musamman da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wadda ke rike da mulki a kasar Sin ta dauka yana bisa hanya, hakan ya sa al'ummun kasar Sin suke cike da imani cewa, za a ci gaba da kafa yankin tattalin arziki na musamman a kasar, kuma za a ciyar da su gaba yadda ya kamata.

Yanzu haka, duniya na fuskantar manyan sauye-sauye, a don haka ya dace birnin Shenzhen ya yi amfani da damar tarihi, ta yadda zai samu karin ci gaba. A cikin jawabinsa, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata a tsaya tsayin daka domin samun ci gaba, ta hanyar yin amfani da shawarwarin kwararru da karfin kirkire-kirkire, kuma ya nuna goyon bayansa ga birnin Shenzhen da ya aiwatar da hadadden gwajin kwaskwarima, domin zama abin koyi ga sauran sassan kasar.

Duk da cewa, kasar Sin tana fuskantar matsaloli yayin da take ingiza gyare-gyare, amma ba ta ji tsoro ko kadan ba, haka kuma za ta ci gaba da yin kokari domin kirkiro sabbin abubuwan al'ajabi wadanda za su amfani sauran kasashen duniya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China