2020-10-14 16:41:14 cri |
Birnin Shenzhen wata alama ce ga kasar Sin a fannin yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje.
Yau shekaru 40 da suka gabata, birnin wani kauye ne da ba a san sunansa ba ko kadan dake kudu maso gabashin Sin, amma yanzu yana sahun gaba a fannoni daban-daban a duniya. Misali ma'aunan tattalin arziki, da karfin kirkire-kirkire, da karfin tattalin arziki, wanda matsayinsa ta fuskar karfin tattalin arziki ya kai matsayi 30 bisa dukkanin biranen duniya, yawan lambar kira ta duniya da yake kirkirowa a kowace rana ya kai 60, kana karfin kirkire-kirkire ya kai matsayi na biyu a duniya.
Shenzhen wani bangare ne kawai dake bayyana ci gaban da Sin ta samu, wajen yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga waje.
Tun daga shekarar 1978 zuwa yanzu, Sin ta kai matsayi na biyu ta fannin karfin tattalin arziki a duniya. Yanzu, ba kayayyakin yadi da wasannin yara yake samarwa kadai ga duk duniya ba, har ma ya shiga sha'anonin dogaro da kimiya da fasaha, masu sayayya na kasashen duniya na amfani da wayar salula ta zamani, da manhajan salula da Sin ta kera. Alkaluman da aka fitar na nuna cewa, ya zuwa karshen shekarar 2019, Sin ta mallaki rabin yawan motoci masu amfani da makamashi mai tsabta da aka sayar a duniya, daga cikinsu kamfanin Tesla ya samu ci gaba mai armashi a kasuwar kasar Sin.
Tsohuwar shugabar IMF Christine Lagarde, ta yaba rawar da Sin ta dade tana takawa wajen samun bunkasuwa ba tare tsayawa ba, da gudunmawar da take bayarwa duniya. Ta ce Sin wata gada ce dake hada duniya da wadata a nan gaba. A cewarta, Sin tana kokarin gina wannan gada a cikin shekaru 40 da suka gabata, ta hanyar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje, kuma ba ita kadai take canjawa ba, har ma ta samarwa duk fadin duniya damammaki masu kyau, har ta zama abin misali ga hadin kan kasa da kasa musamman ma a fannin cinikayya.
Bayan samun bunkasuwa cikin sauri bayan shekaru 40, Sin tana fuskantar sabbin matsaloli yayin da take yin kwaskwarima a gida.
Mataimakin shugaban kwalejin nazari na Bankin Raya Kasar Sin Cao Honghui na ganin cewa, kamata ya yi a rika dudduba kai don samun kyautatuwa. Ana bukatar yin babbar kwaskwarima a fannin yanayin al'umma, da horar da kwararru, da tsai da tsare-tsare masu dacewa da sauransu.
Kasashen waje kuma, na mai da hankali matuka kan hanyar da Sin za ta bi nan gaba. Shin ko kasar Sin za ta ci gaba da aikinta a wannan fanni?
A hakika dai, ana nuna damuwa sosai ga ra'ayin kin dunkulewar duniya, da bangaranci, da zaman 'yan marina, amma Sin tana nacewa kan matsayinta na dunkulewar duniya, da samun bunkasuwa da cin moriya tare.
Fan Hengshan, babban jami'i wanda ya dade yana kula da tsai da tsare-tsare da manufar yin kwaskwarima, yana ganin cewa, Sin za ta nace ga tsai da wani shirin bude kofa ga kasashen waje cikin dogon lokaci.
Karkashin lemar wannan ra'ayi, Sin tana kokarin dogaro da bukatun ciki gida, tare da samarwa sauran kasashe wani yanayi mai kyau na samar da adalci da daidaito, don jawo hankalin kayayyaki da albarkatu a bangarori daban-daban na duniya.
Idan mun dauki sha'anin hada-hadar kudi a matsayin misali, tun lokacin da Sin ta rege sharuddan iznin shiga kasuwanninta a watan Afrilu na shekarar 2018, kasuwar hada-hadar kudin kasar ta fitar da hakikanin matakan bude kofa fiye da 50, matakin da ya gaggauta bude kofa a wannan fanni ga duniya.
A halin yanzu kuma, duk da wahalhalu da Sin take fuskanta daga waje, misali matakan hana shigo da kayayyakin fasaha da kimiya daga kasar da wasu kasashe suke dauka, da hana mu'ammalar masu kimiya da fasaha na kasar Sin, amma idan an yi hangen nesa, ana iya cewa, Sin ba za ta dakatar da manufar yin kwaskwarima a dukkan fannoni a cikin gida, da bude kofa ga waje ba. (Amina Xu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China