Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bayanan karya da 'dan siyasar Amurka ya hada sun tono ainihin dalilin gaza dakile COVID-19 a kasar
2020-10-13 19:25:38        cri

Tun bayan barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, wasu 'yan siyasar kasar Amurka suka fara kirkiro da kuma baza karairayi dake shafar kasar Sin, kwanakin baya, 'dan jam'iyyar republican dake aiki a hukumar kula da harkokin diplomasiyya ta majalisar wakilan kasar Amurka Michael McCaul ya gabatar da wani rahoton bincike, inda ya hada wasu bayanan karya domin shafawa kasar Sin bakin fenti, tare kuma da boye ainihin yanayin gaza dakile annobar COVID-19 da Amurka ke ciki, amma a maimakon haka, rahoton da ya hada ya nuna wa al'ummun kasa da kasa ainihin dalilin gaza dakile annobar a kasar.

Shaidu sun nuna cewa, kasar Sin ta yi nasarar dakile annobar, a ko da yaushe jam'iyyar kwaminis dake rike da mulki a kasar Sin tana mayar da moriyar al'ummu da rayukansu a gaban kome, masanan likitancin kasar sun gano kwayar cuta a cikin kwanaki 8, kuma sun yi nasarar hada maganin tantance kwayar cutar a cikin kwanaki 16, kana ta sanar da bayanan da abin ya shafa ga hukumar kiwon lafiya ta duniya da sauran kasashen da abin ya shafa ba tare da bata lokaci ba, ban da haka ta raba fasahohin da ta samu da sauran kasashe, tare kuma da gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa domin ganin bayan annobar cikin sauri.

A daren ranar 19 ga watan Janairun bana, lokacin da masana suka tabbatar da cewa, kwayar cutar COVID-19 tana bazuwa tsakanin mutane, nan take gwamnatin kasar Sin ta tsai da kudurin kulle daukacin hanyoyin hada birnin Wuhan na lardin Hubei da sauran sassan kasar, daga baya an katse hanyoyin a ranar 23 ga watan, a daidai wancan lokaci, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a wajen kasar Sin mutum 9 ne kawai, a kasar Amurka kuwa, daya ne kacal, amma yanzu adadin ya zarta miliyan 8 a Amurka, kuma abin bakin ciki shi ne, adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar a kasar, ya kai kusan dubu 220, duk da cewa, Amurka tana da tsarin kiwon lafiya mafi inganci a duniya, amma ta gaza shawo kan yaduwar cutar a kasar.

Kamar yadda jaridar The Washington Post ta bayyana, hasarar Amurka ta gaskanta cewa, dalilin da ya sa haka shi ne domin gwamnatin Amurka ba ta dauki matakan da suka dace ba yayin da take fuskantar annobar, wato 'yan siyasar kasar sun fi mai da hankali kan moriyar siyasarsu, a maimakon rayukan al'ummun kasar.

Yanzu ya dace 'yan siyasar Amurka su kara ba da muhimmanci kan yadda za su kubutar da al'ummun kasar daga mawuyancin yanayin da suke ciki, bai kamata ba su bata lokaci kan kirkiro karairayi don neman bata sunan kasar Sin.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China