Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Noman Shinkafa a cikin hamada
2020-10-16 11:21:53        cri

 

 

 

 

 

Jama'a, kun taba ganin gonakin shinkafa a hamada? Watakila kuna cewa wasa ne ba gaskiya ba. Amma a kudancin hamadar Taklimakan da ke jihar Xinjiang ta kasar Sin, hamadar da ta kasance mafi girma a kasar, da gaske ne akwai gonakin shinkafa da fadinsu ya kai kadada 20, kuma kwanan nan malama Buheli Qiemu tare da sauran manoma na kokarin girbin shinkafar da suka shuka.
Malamar ta fito ne daga wani kauyen da ke dab da hamadar Taklimakhan, wurin da ya kasance mafi nisa da teku a duniyarmu. A sakamakon karancin ruwa, mazauna wurin sun dade da noman alkama da masara da auduga da suke iya jure fari, kuma ba su taba yin zaton wata rana za su yi noman shinkafa ba. Yau shekaru uku da suka wuce, mashahurin masanin ilmin noman shinkafa na kasar Sin malam Yuan Longping ya fara gwajin noman shinkafar da ta iya jure ruwan gishiri a wurin, kuma malama Buheli Qiemu na daga cikin wadanda aka dauke su yi wannan aiki. Bisa kokarin da suka yi, ga shi abin mamaki ya faru, inda aka samu girbin shinkafa a wannan wurin dake da karancin ruwa da kuma yawan gishiri. Malama Buheli Qiemu ta kuma yi alfahari da cewa, tana samun albashin da ya kai yuan 5600 a kowane wata, har ta zama mafi yawan albashi a kauyensu.(Lubabatu)
 

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China