Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Farfadowar tattalin arzikin kasar Sin za ta taimakawa kasashe makwabta
2020-10-09 15:55:42        cri

Kamfanin Invesco, daya daga cikin manyan kamfanonin dake sarrafa kadarori masu zaman kansu a duniya, ya bayyana a kwanan baya cewa, farfadowar tattalin arzikin kasar Sin daga illar cutar COVID-19, za ta tallafa wajen farfado da tattalin arzikin kasashen dake makwabtaka da ita.

Invesco ya gano cewa, a lokacin hutu na bikin kafuwar jamhuriyyar jama'ar kasar Sin na tsawo kwanaki 8, yawan mutane da suka yi oda a dakunan cin abinci da yawon bude ido ya kai wani sabon matsayi a tarihi. Jami'in kamfanin mai kula da kasuwar Asiya-Pacific David Chao ya shedawa wakilan kafar CNBC cewa, tattalin arzikin Sin ya farfado sosai, matakin da ya baiwa makwabtanta damammaki masu kyau.

Kafar yada labarai na BBC ta ba da labari cewa, a cikin wannan lokacin hutu, sha'anin yawon shakatawa na cikin gidan kasar Sin na da damar farfadowa zuwa matsayin da yake kafin barkewar cutar COVID-19, matakan ingiza bukatun cikin gida da ba da rangwame a wannan fanni sun sa kaimi ga farfadowar sha'anin bude ido a kasar Sin. Sauran kasashe a nahiyar Asiya kuma, sun karkata bukatansu ga kasuwar cikin gida don kiyaye karfin tattalin arzikinsu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China