Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Ya kamata Amurka ta mayar da hankali kan matsalarta ta nuna bambancin launin fata
2020-10-09 15:08:01        cri

Yanzu kasashen duniya na kara damuwa kan matsalar nuna bambancin launin fata da ake fuskanta a kasar Amurka. A kwanan nan, hukumar kula da hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta shirya wata muhawara kan yaki da ra'ayin nuna bambancin launin fata, inda babbar kwamishinar hukumar Michelle Bachelet da wakilan wasu kasashe, suka yi suka da babbar murya kan ra'ayin nuna bambancin launin fata, tare da jaddada cewa, ya kamata kasashen duniya su gaggauta aiwatar da Sanarwar Durban, a kokarin tabbatar da kare hakkokin zuriyoyin 'yan Afirka. Kafin wannan, shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya taba bayyanawa a yayin babban taron MDD cewar, za a tuna da shekarar 2020 sakamakon dimbin ayyukan yaki da ra'ayin nuna bambancin launin fata da aka shirya a jere, ciki har da zanga-zangar da aka yi a Amurka bisa taken "Rayukan bakaken fata na da muhimmanci", sa'an nan kasarsa tana goyon bayan dukkan kiraye-kirayen da ake yi na bukatar daukar matakai cikin hanzari don kawar da nuna bambancin launin fata. Kafin wannan kuma, kwamitin sulhu na MDD ya taba zartas da wani kuduri, inda ya yi Allah wadai da yadda wani dan sanda a Amurka ya nuna karfin tuwo ga George Floyd, dan asalin Afirka har ya mutu.

Rashin daidaito a tsakanin kabilu daban daban wata babbar matsala ce da Amurka ke fama da ita tun a baya. Amma a cikin watanni da dama da suka gabata, matsalar ta kara tsananta. Mun ga yadda wani dan sanda a Amurka ya kashe George Floyd, da yadda Jacob Blake, dan asalin Afirka ya gamu da shanyewar wani bangare na jikinsa sakamakon harbin da wani dan sanda a Amurka ya yi masa har sau bakwai, da kuma yadda wani dan sanda a Amurka ya kashe Breonna Taylor, 'yar asalin Afirka ba hujja ba dalili. Abin da ya fi kamari shi ne wadannan 'yan sanda na fararen fata masu aikata laifufuka ba a yi musu hukunci ba. Duk wadannan lamuran nuna bambancin launin fata, sun kara ingiza tashin hankali a kasar. A waje daya kuma, Amurkawa 'yan asalin Afirka da Latin Amurka sun fi kamuwa da cutar COVID-19 idan an kwatanta da fararen fata, lamarin da ya kara damuwar da ake nuna wa kan matsalar nuna bambancin launin fata da ake fama da ita a Amurka.

Babu shakka, tsanantar matsalar rikicin kabilanci ta kai matsayin koli a tarihin Amurka. Furfesa Neil Karlen na fannin ilmin zamantakewar al'umma da ke Jami'ar North Carolina ya nuna cewa, zanga-zangar da aka yi bisa taken "Rayukan bakaken fata na da muhimmanci" batu ne na nuna kiyayya mafi tsanani a tarihin Amurka, ganin yadda ta samu masu zanga-zanga mafiya yawa, kuma ake ta yinta har na tsawon lokaci. Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, an yi zanga-zanga a kalla 7750 a wurare kimanin 2000 da ke jihohi 50 da ma Washington, D.C. na Amurka, wadanda suka shafi Amurkawa miliyan 15 zuwa 26 ya zuwa farkon watan Yulin bana. Abin da masu zanga-zangar ke bukata shi ne samun babban sauyi daga tushe a maimakon yin kira kawai. Wasu masana sun taba yin tambaya cikin barin rai, cewar idan Amurkawa fararen fata sun fi kamuwa da cutar COVID-19, shin matakan tinkarar annobar za su sha bamban da na yanzu? Idan mutane sun bar wuraren yin zanga-zangar, ko za su daina nuna kabilanci kuma su ji dadin zamansu yadda ya kamata?

Shaidu sun tabbatar da cewa, za a dauki dogon lokaci matuka kafin a magance matsalar daga tushe. Ko da ra'ayin bainar jama'a na bayyana cewa, yanzu akasarin al'ummar Amurka na nuna rashin jin dadi ga yadda ake nuna bambancin launin fata a kasarsu, amma wasu 'yan siyasar kasar da ke sha'awar kara rura wutar take hakkin bil Adama, daga zukatansu ba su son daidaita matsalar, sai dai ma ta kara tsanani, har ma ba sa zargin masu aikata wannan laifi ko kadan. Abu mai firgitarwa shi ne yadda ake yayata ra'ayin "fararen fata a gaban komai" a Amurka, har ma mukaddashin sakataren tsaron kasar Chad Wolf ya furta cewa, masu tsattsauran ra'ayin "fararen fata na gaban komai" kana sun kasance barazana mafi tsanani a kasar Amurka.

Abin bakin ciki ne ganin yadda wasu 'yan siyasar Amurka marasa kunya ke zargin sauran kasashe bisa hujjar kiyaye hakkin bil Adama, yayin da a nasu bangare, ba su yi komai ba kan yanayin nuna bambancin launin fata da ke tsananta a kasarsu. (Marubuciya: Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China