Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta shiga shirin COVAX a hukumance
2020-10-09 10:50:11        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta amsa tambayoyin da manema labarai suka gabatar mata kan yadda kasar Sin ta shiga shirin allurar rigakafin COVID-19 (COVAX) a hukumance.

Hua ta ce, jiya Alhamis Sin ta kulla yarjejeniya da kungiyar samar da allurar rigakafin cututtuka ta kasa da kasa, domin shiga shirin COVAX a hukumance. Kuma Sin ta yi alkawari cewa, da zarar ta kammala bincike da samar da rigakafin cutar COVID-19, aka kuma fara amfani da ita, za ta samar da alluran ga kasashen duniya, musamman ma kasashe maso tasowa. Kasar Sin ta shiga wannan shiri ne, domin ganin an rarraba allura cikin daidaito da adalci da tabbatar da cewa, za ta samarwa kasashe maso tasowa, tare kuma karfafawa sauran kasashe masu karfin gwiwar shiga wannan shiri. Hua ta ce, ta wannan hanya Sin za ta kara yin hadin gwiwa da sauran kasashe a wannan fanni.

Hua Chunying kuma ta kara da cewa, Sin za ta hada kai da kasashe da suka shiga wannan shiri, don taka rawar gani wajen yakar cutar da kiyaye rayuka da lafiyar jama'a a kasashe daban-daban na duniya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China