Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump ya ce sojojin Amurka dake Afghanistan zasu koma gida zuwa lokacin Kirsimeti
2020-10-08 17:01:07        cri
Shugaban kasar Amurka Donald Trump yace ragowar sojojin kasar Amurkan dake Afghanistan zasu koma gida nan da lokacin bikin Kirsimeti.

Sai dai, mai baiwa Trump shawara a fannin tsaro, Robert O'Brien, ya ce mai yiwuwa ne sojojin Amurka 2,500 zasu cigaba da kasancewa a Afghanistan har zuwa farkon shekarar 2021.

Hare haren da Amurka ta kaddamar a Afghanistan, tun a shekarar 2001, ya yi sanadiyyar kashe rayuka sama da 100,000, wanda ya hada da fararen hula, da dakarun tsaron Afghan, da mayakan Taliban, da sojojin Amurka. Shugaba Trump yana ta duba hanyoyin janye sojojin kasar daga Afghanistan.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China