Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Ghana ya gabatar da bukatar takara a babban zaben kasar
2020-10-07 16:58:05        cri
Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya mika takardar neman takara ga hukumar zaben kasar a jiya, domin neman sake tsayawa takara a zaben kasar da za a yi a watan Disamba.

Idan aka sahale masa, Akufo Addo zai tsaya takara karkashin jam'iyya mai mulkin kasar a karo na 4 tun daga shekarar 2008.

Akwai akalla mutane 15, ciki har da 'yan takara masu zaman kansu, da suka nuna sha'awarsu ta tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben na bana. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China