Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
ECOWAS ta dage takunkuman da ta kakabawa kasar Mali
2020-10-07 16:56:47        cri
Kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afrika wato ECOWAS, ta dage takunkuman da ta sanyawa kasar Mali, biyo bayan kafa gwamnatin farar hula ta rikon kwarya.

Wata sanarwar da kungiyar ta fitar, ta yaba da matakan da aka dauka na mayar da kasar tafarkin demokradiyya, ciki har da nada shugaban kasa da Firaministan riko na farar hula, kamar yadda ta nema bayan an hambarar da mulkin kasar a watan Augustan da ya gabata.

ECOWAS ta kakaba takunkumai kan Mali ne bayan sojoji sun hambarar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita, shugaban kasar da aka zaba karkashin kundin tsarin mulki a tsakiyar watan Augusta, tana mai kira da koma gwamnatin da kundin tsarin mulki ya amince da ita. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China