Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin ya yi bitar nasarorin da kasar ta samu a fannin kare hakkin bil Adama
2020-10-07 16:18:26        cri
Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi bitar manyan nasarorin da kasarsa ta samu a fannin kare hakkin bil Adama, yayin mahawarar kwamiti na 3 na babban taron MDD da ya gudana a jiya Talata.

Zhang ya ce tun kafuwar janhuriyar jama'ar kasar Sin shekaru 71 da suka gabata, Sinawa na ci gaba da bunkasa kasar su, kama daga yin aiki tukuru, da samar da arziki, zuwa yanayi na samun karfi na dogaro da kai. Kaza lika Sin ta taka rawar gani wajen kare hakkokin bil Adama.

Jami'in ya kara da cewa, Sin na aiwatar da manufofi dake sanya al'umma gaban komai, ta kuma fitar da al'ummun ta da yawan su ya kai miliyan 850 daga kangin talauci. Har ila yau mahukuntan kasar na sanya manufar kare rayukan al'umma kan gaba, an kuma aiwatar da tsauraran matakai na dakilewa, da kuma shawo kan cutar numfashi ta COVID-19, ta yadda aka kai ga cimma manyan nasarori a fannin.

A hannu guda kuma, Sin ta rungumi ka'idar kasa da kasa ta adalci da daidaito, tana kuma adawa da tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe, baya ga gudummawa da take bayarwa ga kasashe masu tasowa a fannin martaba doka da oda.

Daga karshe Mr. Zhang ya ce a fannin kare hakkin bil Adama, har kullum akwai dama ta kara inganta ayyuka. Ya ce kasar Sin a shirya take, da ta yi aiki tare da sauran kasashen duniya cikin daidaito, da martaba juna, da gudanar da komai a bude cikin hadin gwiwa, don cimma nasarorin da ake fata, karkashin burin kare hakkokin bil Adama. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China