Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
"Abun al'ajabi na kasar Sin" yana taimakawa yaki da fatara a duniya
2020-10-06 17:31:20        cri

Layukan dogo masu saurin tafiya, wata alama ce ta ci gaban kasar Sin, wadanda suke taimakawa sosai ga ayyukan yaki da fatara a sassa daban-daban na kasar. Alal misali, a gundumar Jinzhai dake lardin Anhui, layin dogon mai saurin tafiya ya taimaki bunkasuwar sana'ar yawon bude ido, har ma ya sa gundumar ta fita daga yanayin talauci.

Halin yanzu, yaduwar annobar COVID-19, yana haifar da babban kalubale ga ayyukan yaki da talauci a duniya. A wajen taron kolin tunawa da cika shekaru 75 da kafa Majalisar Dinkin Duniya da ya gudana kwanan baya, shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya sake kira da a kara maida hankali kan batun neman bunkasuwa a duk fadin duniya. Kana a wajen taron karawa juna sani na "samun dauwamammen ci gaba na MDD nan da shekara ta 2030, da kwarewar kasar Sin kan yaki da talauci" da aka yi ta kafar intanet, mahalarta sun bayyana cewa, kwarewar yaki da talauci ta kasar Sin abun koyi ne, har ma wani jami'in gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ya ce, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa ga ci gaban kasashen Afirka, inda a cewarsa, Afirka ta yaba da salon neman ci gaba na kasar Sin, kana ta koyi abubuwa da dama daga kasar.

A matsayin wata babbar kasa dake sauke nauyi bisa wuyanta, a yayin da take kokarin yaki da talauci a cikin gida, kasar Sin tana kuma taimakawa sauran wasu kasashe wajen yaki da talauci ta hanyoyi daban-daban, ciki har da mu'amalar ma'aikata, da yin nazari cikin hadin-gwiwa, da samar da tallafin fasahohi da sauransu.

A shekarar da muke ciki, annobar COVID-19 tana illata ayyukan rage talauci na kasa da kassa, kuma kasar Sin ta nuna himma da kwazo wajen goya wa kasashe masu tasowa baya, da bada shawarar maida batun bunkasuwa a gaba da komai, da karfafa hadin-gwiwar kasashe maso tasowa.

A nasa bangaren, babban darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin dake Najeriya, Charles Onunaiju ya nuna cewa, halartar ayyukan shawarar "ziri daya da hanya daya", na da babbar ma'ana ga kasashen Afirka wajen farfado da tattalin arziki da neman dauwamammen ci gaba, idan aka samu nasarar yaki da annobar. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China